Ahmed Nuhu Bamalli: Magajin Gari ya zama sabon sarkin Zazzau

Ahmad Nuhu Bamalli

Asalin hoton, ZAZZAU EMIRATES/ FACEBOOK

Lokacin karatu: Minti 3

Sabon sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya shiga Fadar Masarautar Zazzau bayan an naɗa shi a matsayin sarki na 19.

Ɗazu da rana ne gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta naɗa a matsayin sabon sarkin Zazzau.

Ya maye gurbin Mai Martaba Alhaji (Dr.) Shehu Idris wanda ya rasu ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba 2020, bayan ya kwashe shekara 45 yana kan mulki."

Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna tawagar sabon sarkin na Zazzau tana isa fadarsa da ke birnin Zaria.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

A cikin bidiyon, an ga mutane da dama sun yi masa rakiya suna yi masa kirari da san barka.

Tun da farko a sakon da gwamnatin Kaduna ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce "Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19.

"Alhaji Bamalli shi ne sarki na farko daga gidan Mallawa cikin shekara 100 da suka gabata, bayan rasuwar kakansa Sarki Dan Sidi a shekarar 1920," a cewar sanarwar.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Ta kara da cewa: "Malam Nasir El-Rufai ya taya Mai Martaba Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli kan nadin nasa kuma ya yi masa fatan alheri da zaman lafiya a mulkinsa".

Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau kuma jakadan Najeriya a kasar Thailand kafin nadinsa a matsayin sarki.

Ɗa ne ga Nuhu Bamalli, Magajin Garin Zazzau, kuma tsohon minista a Najeriya, wanda ya rasu a 2001.

A makon jiya ne gwamnatin Kaduna ta ce masu zaɓen sarki za su sake tattaunawa domin zaɓen wanda ya dace bayan an soke zaɓinsu na farko saboda "sun cire mutum biyu da ke takara".

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

A ranar 24 ga watan Satumba ne Gwamna El-Rufai ya ce yayin da yake jiran sunaye daga masu zaɓen sarkin Zazzau, yana karanta wani littafi na wani Farfesa farar fata kan zaɓen sabon sarkin Zazzau.

A shafinsa na Twitter, El-Rufa'i ya wallafa hoton bangon littafin da Farfesa M G Smith ya rubuta mai taken "Gwamnati a Zazzau" wanda aka wallafa a 1960.

Gwamna El- Rufa'i ya ce littafin da ke bayani kan zaɓen sarakunan Zazzau daga 1800 zuwa 1950 zai yi masa jagora wajen yanke shawarar zaɓen sabon sarkin Zazzau.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Daga bisani ya samu ƙarin littafai waɗanda ya karanta domin ya samu ƙarin fahimta kan yadda zai yi adalci wajen zaɓen sarkin na Zazzau.

'Lokaci mai wahala'

Tuni manyan mutane cikinsu har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar suka taya sabon sarkin murna.

A sakon da Garba Shehu, kakakin Shugaba Buhari, ya wallafa a shafinsa na Twiter, ya ambato shugaban kasar yana taya sabon sarkin murna.

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

Shugaba Buhari ya yi kira ga Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya zama shugaba na kowa da kowa yana mai cewa "wannan lokaci ne mai wahala don haka ina so ka yi amfani da wannan dama wajen hada kan dukkan jama'ar gidajen da ke iya zama sarki domin ci gaban al'ummarka."

A nasa bangare, Atiku Abubakar, ya taya shi murna sannan ya yi masa addu'ar "Allah Ya ja kwana."

Kauce wa X, 6
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 6