Burj Khalifa: Abubuwan da ba ku sani ba kan ginin da ya fi kowanne tsawo a duniya

Asalin hoton, @burjkhalifa.ae
Tun a ranar Alhamis da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta taya Najeriya murnar shekara 60 da samun ƴancin kai ta hanyar yi wa ginin da ya fi tsayi a duniya da ke Dubai adon hasken lantarki mai launin kore da fari na titar Najeriya, ƴan ƙasar ke ta neman ƙarin sani kan ginin na Burj Khalifa.
BBC ta binciko muku wasu bayanai kan ginin.
Ginin Burj Khalifa a Dubai, ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa yanzu babu wani gini mafi tsayi a duniya kamarsa.
Ginin wanda ya ƙunshi lambu, da otel mai ƙunshe da ɗakunan barci na ƙasaita da kantina, an ƙaddamar da shi ne a 2010 kuma mallakin gwamnatin Daular Larabawa.
Gwamnatin Daular Larabawa ta gina dogon benen ne ƙarƙashin shirinta na janyo hankalin masu yawon buɗe ido da nufin samun kuɗaɗen shiga domin rage dogaro da arzikin fetur.
Ginin ya kafa tarihi da dama a duniya, ta fuskar tsayi da kuma tsarinsa.
Gini mafi tsayi a duniya
Ginin Burj Khalifa a Dubai shi ne gini mafi tsayi a duniya, kuma tun gina shi har yanzu babu wani ginin da ya ƙere shi a tsayi.
Tsawon ginin ya kai mita 829.8, wato girman ƙafa 2,716.5, inda ya doke manyan benaye na duniya kamar dogon ginin Toronto da ake kira CN Tower.
Burj Khalifa yana da hawa sama da 160 - ginin da ya fi yawan bene inda ya sha gaban cibiyar kasuwanci ta duniya - World Trade Center da ke New York.
Yawan lifta da ke cikin Burj Khalifa sun kai 57 baya ga wasu na'urori na ɗaukar mutane zuwa wasu sassa na ginin.
Shekaru nawa aka yi ana gina Burj Khalifa?

Asalin hoton, @burjkhalifa.ae
A shekarar 2004 aka fara gina Burj Khalifa, kuma aka kammala ginin har cikinsa a 2009. Hakan na nufin cikin shekara biyar aka kammala ginin mafi tsayi a duniya.
An yi ginin ne da kankare gaba ɗayansa.
Abubuwan da ginin ya ƙunsa

Asalin hoton, @burjkhalifa.ae
Ginin ya ƙunshi gidaje na ƙasaita da kuma otel-otel da da kuma babban kantin da ake kira Dubai Mall.
Akwai kuma wuraren cin abinci da cashewa a cikin benen da kuma wurin shaƙatawa a bakin ruwa da ake kira tafkin Burj Khalifa.
Akwai kuma wuraren mosa jiki.
Wa ya zana Burj Khalifa?

Asalin hoton, @burjkhalifa.ae
Wani fitaccen mai zane ne Adrien Smith ya zana Burj Khalifa a Dubai. Kamfaninsa ya shahara wajen gina dogayen benaye a Amurka.
Kamfanin mai suna Skidmore, Owings & Merrill da ya zana benen cibiyar kasuwanci ta duniya - World Trade Center da ke New York da Willis Tower, shi ya zana Burj Khalifa.
Wani Kamfanin Koriya ta Kudu ne tare da haɗin guiwar wani kamfanin Belguim da Daular Larabawa suka gina Burj Khalifa.
Shugaban Daular Larabawa Shiekh Khalifa ya ɗauki nauyin kammala ginin bayan kamfanin Emaar na ƙasar da ke ɗaukar nauyin ginin da farko ya shiga matsalar rashin kuɗi, matakin da ya sa aka sauya sunan ginin zuwa Burj Khalifa.
An tsara dogon ginin ne kamar harafin 'Y' kuma wanda zai ɗauki gidaje da otel da wurin shaƙatawa.











