Dubai na shan yabo da suka a wajen ƴan Najeriya a Tuwita

Asalin hoton, Emirates Facebook
Birnin Dubai na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE na ta shan yabo da suka a shafin Tuwita a Najeriya, bayan da aka yi adon fitilu a jikin ginin da ya fi kowanne tsawo a duniya na Burj Khalifa da launin tutar Najeriya na kore da fari a ranar Alhamis.
Ginin Burj Khalifa ya yi hakan ne da nufin taya ƴan Najeriya murnar cika shekara 60 da samun ƴancin kanta daga Turawan Mulkin Mallaka, al'amarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ƴan ƙasar.
An yi ta amfani da maudu'in #Dubai a shafukan Tuwitar Najeriya har sau fiye da 40,000 daga yammacin Alhamis zuwa ranar Juma'a.

Asalin hoton, Twitter
Ana ganin kusan Dubai ne birnin da ƴan Najeriya suka fi rububin zuwa a wannan zamani a duniya, ko dai don yawon buɗe ido, ko kasuwanci ko kuma don zuwa asibiti, inda duk shekara mutane ke kashe miliyoyin kuɗi don zuwa can.
Mutane na ta muhawara kan wannan batu ne a shafukan sada zumunta, inda wasu ke gode da Dubai kan wannan kara da ta yi wa Najeriya yayin da wasu kuwa ke ganin ta yi hakan ne don amfanin haɓakar kasuwancinta.
Ga dai abin da wasu ke cewa:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Aisha Yesufu ta wallafa cewa: ''UAE tana taya Najeriya murna ne saboda Najeriyar na kai mata harkokin kasuwacin da yawa. Mu ma za mu ramawa kura aniyarta idan matan sarkin Dubai da ƴaƴansu suka fara zuwa sayayya ƙasarmu.
''Magana ce ta kasuwanci. Ba wata ƙauna ce ta daban ba!''
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
@globecalls cewa ya yi: ''Ga yadda Dubai ta taya Najeriya murna saboda sun fi kowa morar kuɗinmu.''
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
@EmodiMba ya ce: ''Dubai sun girmama mu. Me ya sa ba za su yi ba, bayan can muke zuwa ko da ciwon wuya muke fama da shi.''
Masu yabo
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
@naijababeex ta rubuta cewa: ''Kafin na ce mu kwana lafiya, ginin Burj Khalifa da ya fi kowanne tsawo a duniya da ke Dubai, an ƙawata shi da adon taya Najeriya murnar samun ƴancin kai. Na sha gaya muku cewa ƴan NAjeriya ba tsararrakinku ba ne.''
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 5
@gloria_adagbon ta ce: ''Mun gode ƙwarai da gaske Dubai! Mun gode da kuka girmama Najeriya.''
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 6
@AhmedG13 cewa ya yi: ''Ga dukkan masu fatan Najeriya ta durƙushe, to Allah Ya sa fatan ya koma kansu a duk inda suke. Mun gode UAE, ga shi ko Dubai ma tana taya mu murnar samun ƴancin kai.''
Alaƙar Najeriya da Dubai
Shekaru da dama kenan da 'yan Najeriya ke niƙar gari zuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa domin yin hutu ko sauran sha'ani.
Ta kai wasu ma kan je takanas don yin bikin aurensu a can, inda ko a shekarar 2019 ma an yi bikin biyu daga cikin mutanen da suka taba yin zaman dabaron wata uku a gidan Big Brother Nigeria, wato Bam Bam da Teddy A.
Hakan ne ya sa alaƙar ƙasashen biyu ta wannan fuska ake ganin take ƙara yauƙaƙa.