Nigeria@60: Waiwaye kan tarihin Hausa da Hausawa bayan shekara 60 da samun ƴancin Najeriya
- Marubuci, Imam Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
Wannan maƙala ce ta musamman da BBC ta rubuta albarkacin murnar cikar Najeriya shekara 60 da samun ƴancin kai daga Turawan Mulkin Mallaka na Burtaniya.
Za mu kawo tarihi na manyan ƙabilun ƙasar uku da suka haɗa da Hausawa da Yarabawa da Igbo Kuma Fulani cikin kwana huɗu a jere.

Asalin hoton, IRENE BECKER
Hausawa na daya daga cikin manyan kabilun Najeriya da suka fi jimawa tare da yin fice musamman a arewacin kasar.
Yayin da Najeriyar ke cika shekara 60 da samun 'yancin kai, za mu yi waiwaye, wanda masu salan magana ke cewa adon tafiya, game da tarihin Hausawa, al'adunsu da sauran muhimman batutuwa da suka shafe su.
Asalin Hausawa
Farfesa Tijjani Muhammad Naniya, wani masanin tarihi da al'adun Hausa a jami'ar Bayero da ke Kano ya bayyana cewa:
"Hausawa wani jinsi ne na jama'a da suka samu kansu mafi yawa a yammacin Afrika, mutane ne da suka kafa garuruwa daban-daban, sannan duk garin da suka kafa suna da jagoranci na sarautarsu.
Ba su samu damar hada kansu wuri guda karkashin tuta daya ba, hakan ya sa ake kiran kowanne da sunan garinsu da kuma sunan sarautarsu.
Abin da ya zo ga tarihi, kasar Hausa na da manyan garuruwa guda bakwai wato inda suka fara zama, wadannan garuruwa sun hadar da Daura da Gobir da Kano da Katsina da Zazzau da Rano da kuma Birom."
Fitaccen masanin tarihin Hausawa, Farfesa Abdullahi Sa'id da almajiransa kamar Farfesa Mahadi Adamu, sun bayyana cewa "asalin Hausawa sun taho ne daga yankin Arewacin jamhuriyyar Nijar, wajen Agadas a yanzu, lokacin da Hamada ta fara buwaya sai neman waje mai danshi da lema da ruwa ya sa wasunsu suka fara sauya matsuguni" suka rika komawa wadancan garuruwa da aka lasabta a sama da ke Najeriya.
"Wadanda suka fara kafa tarihi a cikin Hausawa sune Daurawa da suka bunkasa sai suka janyo hankalin mutane da dama daga mabanbantan wurare ciki harda Larabawa", in ji farfesa Mahadi Adamu.
To masu salon Magana kan ce zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai, ko da al'adunsu suka fara cudanya sai kuma sabbin matsaloli suka bijiro, da suka hadar da yunwa da kuma yake-yake, a nan ne wasunsu suka fara hijira suna kafa wasu garuruwan da kuma sarautunsu, duk inda suka kafa gari sai su nada sarautarsu, da dama suna alakanta sarautarsu da ita Daura, amma wasu ba su alakanta ba.
Farfesa Tijjani Muhammad Naniya ya ce "a wani kaulin kuma ana ganin Hausawa sun samo asali ne daga yankin gabashin Afrika, can wajen Habasha, dalili kuwa shi ne al'adun gargajiya irin na wannan wuri sun zama kusan daya da irin na Hausawa, domin kamar yadda Hausawa ke bautawa rana kafin zuwan musulunci haka su ma suke bauta wa rana, sannan kayan da suke sanyawa ma yafe ne kamar Hausawa, kana gidajensu ma na rufin bunu ne kamar yadda na Hausawa suke.
Sannan har yau har gobe akwai irin wadannan Hausawa a Habasha."
Alakar tarihin Hausa da Bayajidda

Asalin hoton, IMAM
Tarihi ya nuna cewa Bayajidda ya bayyana ne tsakanin karni na 16 zuwa na 19 amma kuma akwai shaidar kasancewarsa a al'adar Hausawa tun cikin karni na 9 zuwa na 10.
Sunansa na asali shi ne Abu Zaid. Amma saboda ba ya jin harshen Hausa sai aka sanya masa Ba-Ya-Ji-Da, wato ba ya jin Hausa a da.
Masana tarihi sun ce Bayajidda ne ya kashe wata macijiya a rijiyar nan ta Kusugu da ke Daura. Macijiyar a wancan lokacin ta addabi mutanen garin inda take hana su dibar ruwa.
Sau daya kacal suke samun damar jan ruwa a mako wato ranar Juma'a, saboda yadda wannan macijiya ta yi kaka-gida a wannan rijiya.
Duk da gargadin da aka yi masa, Bayajidda ya yi kokarin dibar ruwa a ranar Alhamis wato ranar da ba a dibar ruwa, a nan ne macijiya ta harzuko ta so hallaka shi, amma sai ya fille mata kai da takobinsa.
Daga baya ne sarauniya Daurama ta amince ta aure shi saboda bajintar da ya nuna.
An ce Bayajidda na da 'ya'ya uku, na farko shi ne Biram wanda ya haifa da 'yar sarkin daular Borno, sai kuma Bawo wanda ya haifa da Sarauniya Daurama na ukun kuma ya haife shi ne da wata kwarkwara.
Bawo ya haifi 'ya'ya shida kuma tare da kawunsu wato Biram su ne suka mulki garuruwan da ake kira Hausa bakwai wanda suka hada da Daura da Kano da Katsina da Zariya da Gobir da Rano da kuma Biram .

Asalin hoton, Imam
To sai dai farfesa Abdallah Uba Adamu, shugaban jami'ar koyo daga gida ta Najeriya, wanda masanin harshe da al'adun Hausawa ne ya ce "alakanta Hausawa da Bayajidda shafcin gizo ne."
Ya kuma ce "duk mutumin da ba shi da alaka da garuruwa guda bakwai da ke arewacin Najeriya, to ba Bahaushe ba ne. Sai dai a kira shi mai magana da yaren Hausa."
Garuruwan dai su ne birnin Kano da Katsina da Daura da Zazzau da Rano da Gobir da kuma Biram.
Farfesa Abdallah ya kuma yi watsi da batun da wasu manazarta ke fadi cewa Hausa yare ne ba kabila ba, a inda ya ce "Hausawa na da daulolinsu."
To sai dai martanin da farfesa Tijjani Muhammad Naniya na jami'ar Bayero ya yi game da wadannan kalamai na Farfesa Abdallah Uba, shi ne babu wani abu a duniya da ake zancensa ba tare da babu shi ba.
''Duk abin da ka ga ana maganarsa to akwai shi, zan yarda idan aka ce kila an yi karin gishiri, ko kuma an yi wani kuskure a ciki, amma ba wai ace babu shi dungurungum ba''.
Al'adun Hausawa

Asalin hoton, IMAM
Farfesa Tijjani Naniya ya ce Hausawa mutane ne musu tsananin rikon al'adunsu na gargajiya, musamman wajen tufafi da abinci da al'amuran da suka shafi aure ko haihuwa ko mutuwa da sha'anin mu'amala tsakanin dangi da abokai da shugabanni da sauransu, da kuma al'amuran sana'a ko kasuwanci ko neman ilmi.
Tun daga zuwan Turawa har yau, Hausawa suna cikin al'ummomin da ba su saki tufafinsu na gargajiya sun ari na baki ba.
Galibin adon namiji a Hausa ba ya wuce riga da wando musamman tsala, da takalmi fade ko kafa-ciki, da hula kube, ko dankwara, ko dara.
In kuma saraki ne ko malami ko dattijo, yakan sa rawani.
Adon mata kuwa, zane ne da gyauton yafawa, wato gyale da kallabi da taguwa da 'yan kunne da duwatsun wuya wato tsakiya.
Yawancin abincin Hausawa kuwa, ana yin sa da gero ko dawa.
Sai kuma sauran abubuwan hadawa, da na marmari, kamar su wake da shinkafa da alkama da kayan rafi da sauransu.
Yawancin Hausawa Musulmi ne saboda haka yawancin al'adunsu da suka shafi aure da haihuwa da mutuwa duk sun ta'allaka ne da wannan addni.
Haka kuma wajen mu'amala da iyaye ko dangi ko abokai ko shugabanni ko makwabta ko wanin wadannan, yawanci na Musulunci ne. Haka nan sha'anin sana'a da kasuwanci da neman ilmi duk a jikin Musulunci suka rataya..
Sana'o'in Hausawa

Asalin hoton, Pius Ekpemi
Da can sana'a da kusuwanci da neman ilmi suna bin gado ne, wato kowa yana bin wadda ya gada kaka da kakanni. Kuma idan mai sana'a ya shiga bakon gari zai je ya sauka a gidan abokan sana'arsa ne.
Idan ma koyo ya zo yi, zai je gidan masu sana'ar gidansu ne saboda haka kusan kowace sana'a akwai sarkinta da makadanta da mawakanta, kai har ma da wasu al'adu na masu yinta da suka sha bamban da na sauran jama'a.
Hausawa na da sana'oi da daman na gargajiya da suke yi tun fil azal, suna da tarin yawa, amma ga wasu daga cikinsu.
- Kasuwaci.
- Fatauci
- Saka
- Rini
- Farauta
- Jima
- Noma
- Kiwo
- Kira
- Sassaka
- Dukanci
- Gini
- Rinji ko fawa
- Wanzanci.

Asalin hoton, Imam












