Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matashiya ta buɗe jaridar makafi ta farko a Habasha
Wata matashiyar 'yar jarida a Ethiopia ta kaddamar da jaridar makafi wato Braille ta farko a ƙasar.
Jaridar Braille tana bai wa makafi damar karanta ta ta hanyar shafa wasu ɗigo-ɗigo da ke zama tamkar harufa.
Fiyori Tewolde ta daɗe tana aiki a jaridar Addis Zemen ta gwamnatin ƙasar amma daga bisani ta yanke shawarar buɗe jaridar makafi.
Ms Fiyori ta shaida wa BBC Amharic cewa: "Akwai 'yan ƙasar Ethiopia kusan miliyan huɗu da ke da larurar rashin gani kuma na lura cewa ba sa samun labarai - sannan ba sa samun damar sani idan akwai guraben ayyuka waɗanda za a wallafa a jaridu."
Jaridar da ta buɗe, mai suna Fetil (ma'ana "Zare" a harshen Amharic ), za a riƙa wallafa ta duk ranar Laraba kuma za ta mayar da hankali kan labaran mu'amalar yau da kullum, tattalin arziki da siyasa.
Ms Fiyori ta ce za kuma a ware wani shafi na musamman da za a riƙa wallafa labaran bin ƙwaƙƙwafi kan ƙalubalen da mutanen da ke da larura suka fama da su a Ethiopia.
Ta bayar da kwafi-kwafi na jaridar ga ƙungiyar makafi ta Ethiopia, da ofisoshin gwamnati da sauran ƙungiyoyi.
"Muna so idan masu larurar rashin gani sun je irin waɗannan wurare su samu Fetil a kan teburan da ake ajiye jaridu da mujallu domin su karanta," in ji Ms Fiyori.
Ta ce ya zuwa yanzu jaridar ta samu karɓuwa a wuraren jama'a.
Za a riƙa sayar da jaridar a kan titunan Addis Ababa a kan kuɗin ƙasar birr 30 ($0.82, £0.64), wanda ke nuna cewa tana da tsada domin kuwa ta ninka kuɗin da ake sayar da sauran jaridu.
Jaridar ta yi tsada ne saboda yadda ake wallafa ta na musamman ne.