Da gaske an kai wa jirgin ƙasan Abuja hari?

Asalin hoton, Others
A ranar Litinin ne aka fara yaɗa wani labari cewa an kai wa jirgin ƙasan da ke jigila tsakanin Abuja da Kaduna hari, inda har wasu hotuna suka yaɗu a shafukan sada zumunta.
Hotunan dai sun nuna yadda wasu gilasan tagar jirgin suka yi rugu-rugu tare da tarwatsuwa a kan kujerun jirgin.
A wata ruwayar kuma an yi ta cewa har da harbe-harben bindiga aka yi wa jirgin, wasu kuma na cewa karɓe ikon jirgin aka yi.
A kan wannan dalili ne BBC ta yi binciken ƙwaf don jin ainihin abin da ya faru ta hanyar jin ta bakin hukumomi da kuma fasinjojin cikin jirgin.
Ainihin abin da ya faru
BBC ta tuntuɓi manajan da ke kula da jiragen Victor Adamu, inda ya tabbatar da cewa al'amari biyu daban-daban ne suka faru a yammacin jiya ga jirgin da ya tashi daga Abuja zai je Kaduna da kuma wanda ya tashi daga Kaduna zai je Abuja.
Victor Adamu ya ce da farko dai jirgin da ke tafiya daga Abuja zuwa Kaduna ya tashi da misalin ƙarfe 6 na yamma ne, sai wasu mutane suka jefi jirgin da dutse inda har aka fasa gilashin taga ɗaya daga cikin tagogin.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ma ya ruwaito cewa mai magana da yawun ƴan sandan ofishin Rijana, daidai inda lamarin ya faru ya ce jirgin ya isa birnin Kaduna lafiya bayan faruwar lamarin.
Ya kuma ce ba hari ne aka kai ba, wasu ɓata gari ne suka yi jifa da dutse.

Asalin hoton, Getty Images
ASP Mohammed Jalige ya ce: "Ba harbin bindiga aka yi ba, ba kuma kwari da baka ba ne, abin da suka yi jifan da shi ba wani mummunan makami ba ne.
''Ba hari ba ne, jirgin na cikin tafiya abin ya faru. Jami'anmu da ke Rijana sun shawo kan lamarin,'' in ji shi.
Rundunar ƴan sanda yankin ta ce an ƙaddamar da bincike don gano yadda abin ya faru da kuma hukunta duk wanda aka kama da hannu a ciki.
ASP Jalige ya ce: ''Zuwa yanzu dai ba a kama kowa ba amma mun tura jami'anmu yankin don zaƙulo masu laifin.''
Akwai wanda ya ji rauni?
Rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta dai na cewa har fasinja ɗaya ya ji rauni, amma hukumomin da ke kusa da jirgin da ƴan sanda sun ƙaryata wannan labari.
Me ya faru da jirgi na biyu?
Shi kuwa jirgi na biyu da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja ya lalace ne bayan an wuce garin Jere da kaɗan.
Hukumar jirgin ta tabbatar wa da BBC cewa jirgin ya samu matsala ne kuma daga bisani an tura wani kan jirgin ya ja wanda ya tsaya ɗin.
Wasu fasinjoji da ke cikin jirgin sun cewa BBC jirgin bai isa Abuja ba sai da misalin ƙarfe 11 na dare, ''amma baya ga lalacewar da ya yi babu wani abu na firgici da ya faru a jirgin.''
''Mutane dai wasu sun ɗan tsorata ganin cewa a cikin jeji jirgin ya tsaya, amma ganin ƴan sandan da ke ciki masu manyan bindigogi sun ɗan kwantar wa da wasu hankali musamman iri na.,'' in ji wani fasinjan.
Amma wani fasinjan daban ya ce babban abin da ya ɓata masa rai shi ne rashin wata sanarwa daga jami'an da ke kula da jirgin.
''A ƙalla dai idan suna sanar da mu halin da ake ciki ai hankulan mu za su kwanta, amma sun bar kara zube, idan muka je musu da tambaya kuma babu wata taƙamaimiyar amsa da za su ba mu.
''Ai wannan kaɗai ya isa ya sa zuciyoyin wasu su yi kamar za su fito saboda fargabar me zai iya faruwa a daidai wannan lokacin,'' in ji fasinjan da ya buƙaci a sakaya sunansa.
''Ramuwar gayya''

Wani jami'in ɗan sanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce yana tunanin wannan jifa da aka yi wa jirgin Abuja zuwa Kaduna kamar na ramuwar gayya ce.
''A ranar Lahadi wani jirgi ya kaɗe wata saniya har ta mutu kuma a daidai yankin Rijanan abin ya faru. A ganina ba mamaki masu ita ne suka yi wannan jifan na jiya da daddare don rama wannan abu.
''Sai dai kuma abin da ba su sani ba shi ne, shi jirgi ai ba ya tsayawa komai a kan hanya, kuma ba da gangan ya kaɗe saniyar ba,'' a cewar ɗan sanda.
Matashiya
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun irin wannan lamari ba.
A baya can ma an sha jifan jirgin inda gilasansa suka fashe ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, kamar yadda fasinjoji masu yawan bin jirgin da dama suka shaida mana.
Sannan kuma ko batun lalacewar jirgin ma ba wannan ne karo na farko ba, don kuwa ya sha lalacewa a hanyar a wasu lokutan har sai an kawo wani kan ya ja wanda ya tsaya ɗin.











