Tsoron garkuwa na sa jama'a jure wuya a tashar jirgin kasa

- Marubuci, Usman Minjibir
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
Wakilin BBC, Usman Minjibir ya yi rakiya zuwa tashar jirgin Idu da ke birnin Abuja ga kuma rahoton da ya samo mana.
Za a iya cewa idan wani dan Najeriya wanda ya tashi ko kuma yake kai kawo a tsakanin kasashen da suka ci gaba, ka iya zubar da hawaye ganin irin halin da jama'a ke ciki a tashar jirgin kasa ta Idu da ke Abuja.
Watakila kasancewar jirgin kasa a irin wadannan kasashe ba wani kayan gabas ba ne, amma a kasarsa al'amarin ya yi kama da irin abin da Bahaushe ke kira 'wata miyar sai dai a makwabta'.
Na yi rakiya zuwa tashar jirgin ta Idu kuma na ga irin yadda jama'a ke guje-guje da turmutsutsu tun daga neman tikitin har zuwa shiga jirgi. Idan da a ce ban ga me yake faruwa ba da sai na ce halayyar 'yan kasata ne da komai sai an yi gudu da hargowa.
Mun je tashar jirgin da misalin karfe 9:00 na safe wato saura minti kimanin 45 jirgi na biyu ya tashi daga Idu zuwa Kaduna. Abin da ya ba ni mamaki shi ne yadda na ga daruruwan jama'a da suka hada mata da yara kananan suna ta faman karakainar neman tikiti.

Wasu sun samu irin wanda suke so. Wasu kuma sun kare a samun tikitin da ake kira 'Standing' wato mutum zai kwashe kimanin awa biyu yana tafiya a tsaye a cikin jirgin. Da dama wasu kuwa sun gwammace jiran jirgin karfe biyu inda suka samu wuri suka zauna.
Sai dai wasu da na samu zanta wa da su amma ba su ba ni iznin ambatar sunansu ko kuma daukar hotonsu ba sun shaida min cewa sun fasa tafiyar.
Wata mata wadda na rinka lallashinta ta yi rantsuwa cewa "ni da dawo wa wurin nan har abadan wallahi. Na gwammace na hau mota duk abin da zai faru da ni ya faru. Da ma ai Allah ne yake kiyaye mu ba wayonmu ba."
Ta shaida min cewa za ta je Kano ne domin ziyartar 'yan uwa da abokan arziki kuma ta ce "da ikon Allah ba fashi sai na je Kano a yau din nan". Mun kuma rabu da ita inda ta nemi mai tasi domin ya kai ta tashar mota ta Jabi da ke Abujar domin daukar hanyar Kano.

Na kuma hadu da wani matashi mai suna Yusuf wanda ya nemi da na rage masa hanya daga tashar jirgin zuwa cikin garin Abuja.
Yusuf wanda mazaunin Abuja ne ya shaida min cewa bai samu kujera a jirgi ba sai 'Standing' wato tsayuwa a cikin jirgi, inda ya ce yana fama da larurar ciwon kafa, shi ya sa ya fasa tafiyar.
To sai dai ba kamar baiwar Allar da na hadu da ita ba, Yusuf ya koka da matsalar tsaro da ta dabaibaye hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda ya ce "idan ban da matsalar tsaron nan ai da yanzu na kai Kaduna a motata."
Yusuf cikin fushi, ya shaida min cewa ya kamata a sahhale wa 'yan kasa iznin mallakar bindiga ko kuma daukar hayar jami'an tsaro a motocinsu ko kuma na haya domin yin ba-ta-kashi da masu garkuwa da jama'a.
Daga karshe Yusuf ya ce "abin takaici ma shi ne yadda za ka zo kana wahalar neman tikiti amma sai ka ga manyan sojoji da 'yan sanda da sauran jami'an gwamnati sun zo sun samu tikitin ba tare da wata wahala ba. Ka ga ke nan batun tsaro babu ranar da zai gyaru tun da wadanda ya kamata su ba ku tsaro su ma suna ta kansu. Allah ya kiyaye."
Wani abin da ya bai wa Yusuf da sauran mutanen da suke zuwa tashar jirgin ba tare da samun biyan bukata ba shi ne irin wahalar da tsadar da ke tattare da daukar tasi daga cikin Abuja zuwa tashar Idu da ke cikin lungu.
Yayin da Yusuf da wannan baiwar Allah suke baro tashar jirgin da bacin rai, ni kuwa na fito da murnar mutanen da na yi wa rakiya tuni suka samu tikitin tsayuwa a jirgi wato 'standing' zuwa Kaduna. Domin bukatar maje haji, Hausawa sun ce Sallah.
















