An kaddamar da jirgin kasa mafi gudu a Nigeria

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kaddamar da sabon jirgin kasa na fasinja wanda zai dinga zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna a wani kasaitaccen biki a ranar Talata.
A yayin bikin kaddamarwar, shugaban ya yi tafiyar minti 18 a jirgin daga tashar Idu zuwa ta Kubwa tare da dumbin jama'a.
- <link type="page"><caption> Hotunan kaddamar da jirgin kasa mafi gudu a Nigeria</caption><url href="http://www.bbc.com/hausa/multimedia/2016/07/160726_picgallery_nigeria_launches_speed_train.shtml" platform="highweb"/></link>Za mu kawo muku karin bayani nan ba da jimawa ba.
Daga nan sai jirgin ya wuce birnin Kaduna a tafiyar kilomita 120 zuwa 150 a duk sa'a daya.
Za a dinga cajin fasinjojin jirgin naira 500 daga Abuja zuwa Kaduna.
Jirgin shi ne irinsa na farko mafi gudu da aka kaddamar a Najeriya, kuma yana yin tafiyar sa'o'i biyu ne tsakanin Abuja da Kaduna.
An bayar da aikin kwangilar jirgin ne tun zamanin mulkin shugaban Cif Olusegun Obasanjo, amma sai a lokacin shugaba Jonathan aka kadaamar da aikin, duk da cewa bai fara aiki a lokacin ba sai a yanzu.
Wannan dalili ne yasa jam'iyyar adawa ta PDP wadda ita ce ta tsohon shugaba Jonathan din take ta wallafawa a shafinta na Twitter cewa a karkashin mulkinta ne aka yi wannan ''hobbasa''.
Ta kuma ce shugaba Buhari ya samu damar kaddamarwar ne kawai amma ba ''kokarinsa'' ba ne.










