Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pierre-Emerick Aubameyang: Mikel Arteta yana so magoya bayan Arsenal su kwantar da hankalinsu
Magoya bayan Arsenal za su iya "kwantar da hankalinsu" a kan kwangilar Pierre-Emerick Aubameyang ganin cewa ba a kammala musayar 'yan kwallon wannan kakar ba, a cewar Mikel Arteta.
Arteta yana da "kwarin gwiwar" cewa kyaftin din na Arsenal zai sabunta kwangilarsa.
Kwangilar Aubameyang za ta kare a bazara mai zuwa, abin da ya sa ake hasashen cewa zai bar kungiyar, amma a watan jiya Arteta ya ce ya rarrashe shi ya zauna.
"Yana cike da farin cikin zamansa a nan," in ji Arteta, da yake magana kafin fafatawarsu da Fulham ranar Asabar.
"Yana so ya ci gaba da zage damtse ya taimaka wa kungiyar. Ina ganin ya kamata magoya bayansa su kwantar da hankalinsu."
A wannan bazarar Arsenal ta sayi dan wasan Brazil Gabriel Magalhaes a kan euro 26m daga Lille, ta sake dauko tsohon dan wasan Chelsea Willian sannan ta sake karbo aron Dani Ceballos daga Real Madrid.
Kazalika ana sa ran za ta dauko dan wasan Atletico Madrid Thomas Partey da dan wasan Lyon Houssem Aouar.