Zan rike Aubameyang komai rintsi — Arteta

Mikel Arteta ya ce Arsenal za ta rike Pierre-Emerick Aubameyang ko ta wane hali domin ya ci gaba da zama a Emirates.

Kocin na Arsenal ya ce za su zauna da dan wasan na tawagar Gabon kafin karshen kakar nan, domin tsawaita yarjejeniyar kyaftin din.

Kwantiragin Aubameyang zai kare ne a karshen kakar 2020-21.

Aubameyang, mai shekara 30, ya ci kwallo 20 a fafatawar da ya yi wa Gunners a bana, ana kuma cewa Barcelona da Inter Milan za su yi zawarcinsa.

Arteta ya ce ''Tabbas Arsenal za ta zauna da dan kwallon Gabon kan tsawaita zamansa a Gunners kan karshen kakar bana.

''Amma makomar tattaunawa da Aubameyang za ta ta'allaka kan kokarin Gunners a karshen kakar shekarar nan ''.

Arsenal tana mataki na 10 a kan teburin Premier da maki takwas tsakaninta da ta hudu Chelsea.

Arsenal ta fice daga gasar Zakarun Turai ta Europa League a karawar zagaye na biyu, bayan da Olympiakos ta yi nasara a kanta.