Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ba za ta yi siyayya a Janairu ba — Arteta
Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce bai jin zai sayo 'yan kwallo a watan nan na Janairu.
Gunners tana mataki na 10 a teburin Premier, maki tara tsakaninta da Chelsea wadda take da hudu a teburi.
Arteta ya karbi aikin horas da Arsenal a watan jiya, kawo yanzu ya ci wasa biyu da canjaras daya da rashin nasara a fafatawa daya.
''Idan za mu iya samun wanda zai taimaka mana a gurbi ko wani wuri na musamman zan iya neman zabi'' in ji Arteta.
''Amma dai bana tunanin zan sayo dan wasa kawo yanzu a Janairun nan.
A bana ne Arsenal ta fitar da kudi ta dauki dan wasa mafi tsada a tarihinta Nicholas Pepe kan fam miliyan 72.
Haka kuma kungiyar ta dauki Kieran Tierney kan fam miliyan 25 da David Luiz da kuma Gabriel Martinelli .
A dai banar Gunners ta dauki aron William Saliba daga Saint-Etienne, inda kudin sayo 'yan wasan ya kai fam miliyan 135 jumulla..
Arteta ya ce zai bayar da aron Emile Smith Rowe da Eddie Nketiah da kuma Tyreece John-Jules a watan nan.