Ko kwalliya na biyan kuɗin sabulu kan yawan cin bashin da Shugaba Buhari ke yi?

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Tsakanin shekaru biyar na mulkin Buhari, bashin Najeriya ta ƙaru da kusan tiriliyan 19.

Yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai sama da naira tiriliyan 31 daga ƙarshen watan Yuni, kamar yadda ofishin kula da basussuka a Najeriya ya sanar.

Ofishin ya bayyana a cikin rahoton da ya fitar ranar Laraba cewa yawan bashin ya ƙaru da naira tiriliyan 2.38 tsakanin wata uku.

Yawan bashin ya shafi wanda jihohi da gwamnatin tarayya suka karɓo. "Alƙalumman sun nuna cewa a naira - jimillar bashin na gwamnatin tarayya da jihohi 36 haɗi da Abuja ya kai naira tiriliyan 31.009 kwatankwacin dala biliyan 85.897.

Bashin ya ƙaru ne saboda rancen dala biliyan 3.36 da gwamnati ta karɓo daga asusun lamuni na duniya IMF da kuma rance daga cikin gida don tallafawa kasafin kuɗi na shekarar 2020 da aka sabunta.

Daga ƙarshen 2015, bashin naira tiriliyan 12.12 ake bin Najeriya, makwanni bayan hawan gwamnatin APC ta shugaba Buhari.

Hakan na nufin tsakanin shekaru biyar na mulkin Buhari, bashin Najeriya ta ƙaru da kusan tiriliyan 19.

Ofishin kula da basussuka a Najeriya ya ce yawan bashin zai ƙaru yayin da ake jiran kuɗaɗen rance daga Bankin Duniya da Bankin raya Afirka da kuma Bankin musulunci domin tallafawa kasafin kudin Najeriya na 2020 musamman wanda ƙasar ta nema sakamakon tasirin annobar korona.

Haka kuma kuɗaɗen da ake bin jihohi zai ƙaru daga sabon rancen da suka nema.

Masana tattalin arziki kamar su Yusha'u Aliyu suna ganin bashin da Najeriya ta ci yana da yawa kuma duk da yana da matsala ga tattalin arziki amma kuma yana da tasiri, kamar yadda suke ganin akwai dalilai da ya yawa na karɓo rancen kamar haka:

  • Gwamnatin APC ta tarar da bashi mai yawa duk da bai kai yadda bashin yake a yanzu ba.
  • Kudaden da ake saka wa a kasafin kuɗi da ake biyan basussuka - bashin na ƙaruwa kuma kuɗaden na ƙaruwa
  • Kasafin mai girma ne kuma mai giɓi, wanda ya sa dole sai an nemo kuɗade
  • Hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na gwamnati wanda ya dogara da man fetur, sai ga shi kuma farashin fetur ɗin ya yi mugunyar faɗuwa.
  • Jihohi sun yi ƙarin albashi kuma sun rasa kuɗin biyan albashin wanda ya tilasta masu ciwo bashi.
  • Annobar korona da ta kara taɓarɓarewar tattalin ariki
Kudin Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Masana na ganin duk kasafin kuɗaden da ake biyan bashi a cikinsa yana sarkafe harakokin ci gaban tattalin arzikin da ke cikinsa.

Kuma har yanzu kasafin kuɗin Najeriya yana da giɓi wanda ake ganin yana da wahala kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Yawan basukan ya sa gwamnati ta ke neman hanyoyin da za ta samu kudi, shi ya sa ta ke ta ƙarin haraji ana cire tallafi don samun kudaden da za su taimakawa gwamnati.

"Hukumomin da ke bayar da bashi sun lurar da Najeriya kan yawan bashin da ta ke karɓa wanda idan har ƙasar ta ci gaba da karɓa, girman bashi zai hana ta samu wasu kuɗaɗen rancen a nan gaba," in ji msanin tattalin arziki Yusha'u Aliyu.

Ya kuma ce babban matsala ce gwamnati ta raja'a ga yawan karɓo bashi domin biyan buƙatunta saboda kuɗaɗen da za a dinga biyan basussukan zai yi wa tattalin arzikin naƙasu.

A cewarsa, tun da farko gwamnati ta yi sakaci aka bari naira ta karye bayan rufe ƙofofin taimakonta ta hanyar ajiye kuɗaɗe a ƙasashen waje duk da ana buƙatarsu a cikin gida - "wannan ne ya haifar da hauhawan farashin kayayyaki a ƙasar."

"Da zarar hauhawan farashi ya shigo tattalin arziki, to duk kudaden da ke cikinsa za su tafi da hauhawan farashin ne saboda duk farashin da ke kasafin kudi za a auna shi da darajar naira ne tsakaninta da dala a daidai wannan lokacin," in ji shi.

Tasirin yawan bashi ga tattalin arziki

Masana na ganin yawan bashin da ƙasa ke karɓa yana iya tasiri ga ci gaban manufofinta ko kuma haifar da tarnaƙi ga ci gaban da ake fatan cimma.

Babbar illa shi ne yadda za a dinga ware kudade masu yawa da ya kamata a zuba wajen gina tattalin arziki amma sai karkatar da su wajen biyan bashi.

Haka kuma sauran harakokin ci gaban ƙasa za a tsayar da su saboda babu isassun kuɗi da za a gina tattalin arziki ba musamman idan gwamnatocin jihohi suka kasa karkata zuwa wasu fannoni na samun kuɗaɗen shiga ba.

Kuma duk kasafin kudin da aka yi kuma aka ware wani kaso mai tsoka domin biyan basuka daga cikin ksafin kudin, babbar illa ce ga ci gaban tattalin arziki.

Girman gibin da ke cikin kasafin kuɗi babbar masana na ganin matsala ce ga ayyukan ci gaba na samar da sabbin ayyukan yi da bunƙasa noma da wutar lantarki da kuma gina hanyoyi saboda maimakon ayyukan za a ware kuɗaɗen ne ana biyan bashi.

"Yawansa da tsawonsa zai sa a daɗe ana wahala a Najeriya musamman idan ba a yi tanadi kan wasu abubuwan da za su iya tasowa kamar annobar korona.

Wannan layi ne

Karin labarai da za ku so ku karanta: