Tsadar rayuwa a Najeriya: Shin ₦30,000 za ta iya magance matsalolinku?
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Karin farashin man fetur da na hasken wutar lantarkin da aka yi a Najeriya sun sake jefa 'yan kasar a mawuyacin hali.
Hakan na faruwa ne a yayin da suke cikin karin matsin tattalin arziki sakamakon annobar korona wacce ta tilasta wa duniya zama cikin dokar kulle.
Sai dai gwamnatin kasar ta bayyana dalilai da suka sanya tsadar rayuwa a kasar.
BBC Hausa ta yi nazari yadda 'yan Najeriya, wadda gwamnatin tarayyarta take biyan ₦30,000 a matsayin mafi karancin albashi, za su yi amfani da wannan adadi wajen gudanar da rayuwarsu a wannan mawuyacin hali da ake ciki.