Ambaliyar ruwa a Najeriya: Sama da gidaje dubu 50 sun rushe a jihar Jigawa

Yadda gidaje ke rushewa a Jigawa
Bayanan hoto, Yadda gidaje ke rushewa a Jigawa

Hukumomi a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum goma sha tara sannan fiye da gidaje dubu hamsin sun rushe sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliyar ruwa a sassan jihar.

Lamarin dai ya haddasa salwantar dukiyoyi a kananan hukumomi goma sha bakwai daga cikin ashirin da bakwai na jihar.

Al'amarin dai na zuwa ne bayan shafe makwanni ana tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Al'umomin garuruwan Babaldu da Shingurin da Samamiya da ke yankin karamar hukumar Birnin Kudu a jihar ta Jigawa, na cikin tsaka mai wuya sai dai lamarin ya fi muni a garin Shingurin wanda yanzu haka wani kogi da ya tumbatsa ya tasamma tashin garin ɗungurungum.

Baya ga rusa gidaje da lalata amfanin gona, har rasa rai wannan iftila'i ya haddasa inda wani matashi ya rasa ransa a garin na Shingurin.

Ruwan sama ya haddasa ambaliyar ruwan data lalata amfanin gona a Jigawa
Bayanan hoto, Ruwan sama ya haddasa ambaliyar ruwan data lalata amfanin gona a Jigawa

Alhaji Umar Aliyu shi ne mahaifin matashin ya kuma shaida wa BBC cewa, yaaon nasa ya je kai taimako ne gidan kanin mahaifin nasa a nan ne kuma sai gini ya rufta masa anan ne kuma sai ya nitse a ruwan da ya zama kamar kogi.

Mahaifin matashin ya ce "Tun da ruwa ya tafi da shi ba a ganshi ba sai bayan kwana hudu, sannan aka gano gawarsa a wani gari can daban".

A yanzu haka dai daruruwan iyalai ne wadanda suka tsira daga gidajen su suka sami mafaka a gidajen 'yan uwa da makarantu da masallatai, yayin da wasunsu kuma suka ci gaba da zama a gidajen nasu duk da mamayewar da ruwan ya yiwa ciki da wajen gidajen nasu.

Malam Abubakar Garba Haske na daga cikin mutanen da suka rasa gidajensu ya kuma shaida wa BBC cewa, "Yanzu a makaranta nake kwana, muna da gidajenmu da wasu kayan abincinmu duk sun lalace, kai hatta tufafinmu duk sun lalace saboda tsabar ruwan sama wanda ya yi sanadin rushewar gidajenmu".

Wannan layi ne

Kwana a makarantu da masallatai

Yadda mutane suka koma kwana a makarantu saboda rushewar gidajensu a Jigawa

Wakilin dagacin Shingurin Malam Alhassan Abdu, ya ce bai taba ganin iftila'i irin na wannan shekarar ba, komai da suka shuka na amfanin gona ruwan ya lalata.

Alhaji Yusuf Sani Babura, shi ne shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Jigawa, ya kuma shaida wa BBC cewa, babban abin da ya fi tayar musu da hankali yanzu shi ne irin yadda gidaje ke rushewa akasari a kauyuka.

Ya ce "A yanzu muna adadin gidajen da muka tabbatar sun rushe saboda ruwan sama a sassan jiharmu sun kai sama da dubu hamsin da daya, sannan kuma muna da labarin cewa akwai wadanda ke kwana a makarantu da masallatai saboda rashin matsunni".

Alhaji Yusuf Sani Babura, ya ce ba su da labarin abin da ya faru a Shingurin don ba a kawo musu rahoto ba, to amma tun da yanzu sun samu rahoton iftila'in da suka shiga, za a kai musu dauki na gaggawa.

Wannan layi ne
An sha samun ambaliya a wasu sassan jihar Jigawa

Asalin hoton, The Guardian

Bayanan hoto, An sha samun ambaliya a wasu sassan jihar Jigawa

Ba wannan ne karon farko da ake samu ambaliyar ruwa da rusau na gidaje a jihar Jigawa ba, ko a bara ma an samu irin wannan matsala a wasu kauyuka dama cikin kananan hukumomin jihar kamar karamar hukumar Buji, wadda a yanzu haka yadda ruwan saman ya mamaye garin Gantsa ya fi na bara barna ma.

Kazalika ana yawan samun ambaliyar ruwa a sassan arewacin Najeriya a duk shekara sakamakon ruwan saman da ake shekawa kamar da bakin kwarya.

A wasu lokutan dai cushewar magudanan ruwa da kuma yadda wasu ke zama a wuraren da ruwa ke wucewa na daga cikin matsalolin da ke kara ta'azzara ambaliyar ruwan musamman a lokacin damuna.

Abin tambayar anan shi ne, shin me gwamnatoci keyi wajen dakile irin wannan sake afkuwar irin wannan matsala a gaba?

Wannan layi ne