Saudiyya: Uƙubar da na sha a ƙasar kan zargin shigar da ƙwaya – Alaramma Ibrahim

Gwamnan Zamfara Matawalle a farko, sai Alaramma Ibrahim a tsakiya

Asalin hoton, Hudu Yahaya

Bayanan hoto, Gwamnan Zamfara Matawalle a farko, sai Alaramma Ibrahim a tsakiya

Malamin nan da hukumomin Saudiyya suka kama bisa zargin safarar ƙwaya zuwa ƙasar, amma aka wanke shi daga baya wato Alaramma Hafiz Ibrahim Ibrahim Abubakar, ya bayyana irin halin zullumin da ya shiga a lokacin da aka tsare shi.

A tattaunawarsa da BBC, Alaramma Ibrahim, ya bayyana abin da ya faru inda ya ce, ya yi tafiya ne zuwa Umarah, bai san hawa ba bai san sauka ba sai aka zo aka kama shi.

Ya ce masu gabatar da ƙara a ƙasar sun tuhume shi a kan cewa ya shiga da ƙwaya zuwa ƙasar, amma kuma duk shari'ar da aka rinka yi ba a same shi da laifin hakan ba.

"Masu gabatar da ƙarar suka rinƙa ɗaukaka ƙara, kuma duk inda aka je ba a samu na da laifin hakan, su suna so ne a yanke mini hukuncin kisa".

Ya ce tun farko da aka kama ni sai da na zauna a gidan kaso na tsawon shekara guda da wata biyu kafin ma a gabatar da ni gaban kotu inji Alaramma Ibrahim.

Malamin ya ce rashin gabatar da shi ɗin kuwa na da nasaba da rashin wata ƙwaƙwarar shaida a kan abin da ake zarginsa da aikatawa.

Ya ce, "A lokacin da nake jiran shari'a na shiga zullumi sosai saboda abu ne da ake maganar kisa, to dole ne gaskiya mutum ya damu, domin laifi ne aka ce nayi bayan ni kuma ban san da shi ba, don ita kanta jakar tawa har na baro Saudiyya ban ganta da idona ba.

"Sannan kuma ina wajen da ake ɗaukar mutane aje a kashe su saboda hukuncin da aka yanke musu na kisa, wannan ba ƙaramin tayar mini da hankali ya yi ba," in ji Alaramma Ibrahim.

"Wani abu da na yi yaƙini da shi, shi ne a kullum na san zan kuɓuta saboda abu ne da ni na san ban aikata ba."

Ya ce, da ikon Allah yana zaune Allah ya taimake shi da taimakon gwamnan jihar su na Zamfara aka ba shi lauyan da ya kare shi har kuma aka samu nasara a shari'ar tasa ya kuɓuta daga hukuncin kisa.

Malamin ya ce, sai da ya zauna a ƙasar tsawon shekara fiye da uku kafin a kammala shari'ar tasa, amma kuma ba duka wannan lokaci ya ɗauka a tsare ba.

Ya ce, ofishin jakadancin Najeriya a Saudiyya ya karɓi belinsa sannan ya ci gaba da yi masa duk wasu buƙatu a kasar, sai dai kuma a kullum a cikin zullumi yake saboda bai san makomarsa a kan shari'ar da ake masa ba.

''To amma Alhamdulillahi, gashi a yanzu an wanke ni daga abin da aka zarge ni da aikatawa, sannan har na dawo ƙasata gani kuma a jihata, ga kuma ni tare da iyalaina.

"Dukkan godiya ta tabbata ga Allah (SWA) da ya kuɓutar da ni, don haka ni ko sha'awar zuwa ƙasar ma a yanzu kam bani da ita ba mamaki ko sai nan gaba," in ji Malamin.

Wannan layi ne

Karin bayani

Gwamnan jihar ta Zamfara Bello Matawalle, ne ya karɓi Alaramma Ibrahim, bayan ya ceto shi daga Saudiyya.

Kuma tuni ya bashi muƙamin mai ba shi shawara a kan harkokin da suka shafi karatun Al-Qur'ani.

Yanzu haka dai Alaramma na gida cikin iyalansa, ba kuma ya marmarin zuwa kasar Saudiyya a yanzu haka a cewarsa.

Wannan layi ne