Wasika daga Afirka: Abin da ya sa 'yan ƙasar Kenya ba sa son kundin tsarin mulkinsu

A jerin wasikun da muke samu daga yan jaridar Afrika, Waihiga Mwaura ya yi duba na tsanaki kan sauye-sauyen da aka samu shekaru goma, bayan fara aiki da sabon kundin tsarin mulkin Kenya da aka amince da shi da zummar kawo sauyi a tsarin tafiyar da gwamnati da kuma kawo karshen rikicin kabilanci.

Akwai muhimmin darasi a fitaccen littafin marubucin nan George Orwell mai suna (Gandun Dabbobi), wanda a ciki dabbobin da suka yi wa iyayen gidansu tawaye da zummar kafa 'yantaccen gandu suka kare da da-na-sani, saboda yadda reshe ya juye da mujiya.

Shekaru goma bayan rubuta sabon kundin tsarin mulkin, akwai kwarin gwiwar cewa kasar za ta cimma wanan muradi.

An shafe gwamman shekaru da wannan fata, to amma sai ya kasance an samu wasu 'yan siyasar cikin gida a kasar da suka maye gurbin 'yan mulkin mallaka wajen hana ruwa gudu.

Wannan dalili ne ya sa al'ummar Kenya suka ji kamar su zuba ruwa a kasa su sha ranar 27 ga watan Agustan 2010, lokacin da aka amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Kamar yadda tsohon alkalin alkalan kasar Willy Mutunga ya ce, "Sabbin dokokin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar sun kunshi manufofin da ake so a cimma na shekara da shekaru da aka kwashe ana gwagwarmaya ciki har da wadanda suka jibanci tattalin arziki, da walwalar jama'a da inganta tsarin siyasa da kuma ciyar da al'adu gaba".

Rabon ikon fada-a-ji

Wadanne sauye-sauye sabon kundin tsarin mulkin ya kawo?

E to, a baya kusan shugaban kasa ne ke da karfin ikon yin komai, ciki har da ikon fada-a-ji a kan dukkanin bangarori.

Shi yake nada alkalai, kuma yake da ikon sauke su.

Shi yake da ikon tsara jadawalin aikin majalisa, sannan yana da ikon nada ko ministoci nawa yake so.

Kun dai fahimta.

Sai dai su al'ummar Kenya sun san me suke so sarai !.

Suna son a bai wa kowanne bangare ikon kashin kansa, musamman tsakanin bangaren zartarwa, da majalisa da kuma na shari'a.

Suna son a karfafa hakkokinsu, da kuma tabbatar da daidaito ga jinsin maza da mata.

Sannan suna da ra'ayin karkasa albarkatun gwamnati ga dukkanin yankunan kasar 47 da kundin tsarin mulkin na 2010 ya samar.

Sakamakon kuri'ar jin ra'ayin jama'ar Kenya da kungiyoyin fararen hula suka gudanar ya nuna cewa mutanen kasar da da sabanin ra'ayi.

Kaso 23 cikin 100 ne kacal suka gamsu da yadda ake aiwatar da kundin tsarin mulkin zuwa yanzu, yayin da kaso 77 cikin 100 suka ce walau basu gamsu ba ko kuma ko a jikinsu.

Ba da jimawa ba ne alkalin alkalan Kenya Dabiv Maraga ya ce: "A ra'ayina, kundin tsarin mulkin Kenya na daya daga cikin wadanda suka fi tsaruwa a duniya, amma sai in har za mu rika aiwatar da abin da ya kunsa".

Wani kwararren lauya Ahmednasir Abdullahi kuwa na da ra'ayin cewa kundin ya fifita masu fada-a-ji, yana cewa sun shigar da abubuwan da za su gamsar da su ne kawai ciki.

Daya daga cikin gagarumar gazawar da aka samu ita ce wajen samar da daidaito tsakanin maza da mata a majalisa, domin fiye da kaso biyu cikin uku na 'yan majalisar maza ne.

Banganren shari'a a kasar ya ce ba'a ware masa kason kudin da aka yi masa alkawari a kudin tsarin mulkin.

Sannan ba a yi wata ganawar ido da ido tsakanin bangaren shari'a da zartarwa ba, tun bayan soke zaben zaben shugaban kasa na shekarar 2017 da kotun kolin kasar ta yi, saboda kura-kuran da aka tafka yayin zaben.

Yayin da kotun koli ke shirin sake sauraron wata shari'ar don jinkirta gudanar da sabon zabe bayan soke na farko a 2017, wasu daga cikin alkalan kotun koli basu halarci zaman da aka yi ba.

Daya daga cikinsu bata je kotu ba, saboda bindige wani mai tsaronta da yan bindiga suka yi.

Sannan alkalan na zargin jami'an gwamnati da raina bangaren shari'a, ta hanyar kin bin umarnin kotu.

Har yanzu matsalar tattalin arziki na zaman gagarumar matsala a Kenya, inda yanzu 'yan kasar suka mayar da hankali kan zargin satar miliyoyin dalolin da aka ware don yaki da annobar korona.

Sannan akwai damuwa da wasu ke nunawa kan cewa kundin tsarin mulkin bai bai wa 'yan sanda cikakken ikon cin gashin kai ba.

Sai dai wasu, ciki har da jagororin jam'iyyar hamayya ta ODM kamar Raila Odinga, wanda ya taba zama Firaiminista a gwamnatin gamin bambiza bayan tashin hankalin da aka samu bayan zabe, na ganin cewa akwai bukatar yi wa wasu dokokin kwaskwarima.

Ya hada hannu da shugaba Uhuru Kenyatta wajen cimma wasu manufofi da aka kira da 'Ciyar da kasa gaba''.

Yan hamayyar biyu sun sasanta da juna shekaru biyu da suka gabata bayan sake samun wani tashin hankali bayan zabe.

Sun amince su samar da wata tawaga da zata lalubo bakin zaren warware matsaloli da dama, da suka hadar da rikicin kabilanci, da cin hanci da rashawa da rabon albarkatun gwamnati.

Ba da jimawa ba ne ake sa ran tawagar za ta saki sakamakon rahotonta na karshe.

Sai dai wani sakamakon jin ra'ayin jama'a da aka gudanar ya nuna cewa kaso 60 cikin 100 na 'yan kasa basa ra'ayin sake nazartar kundin tsarin mulkin, yawancin su na da ra'ayin cewa a tsaya a mutunta wanda aka sauya tun 2010.

Sun fi gane cewa 'yan siyasa su yi jagoranci bisa dokokin da ake da su, sun amince da fadin marubucin nan na Russia Leo Tolstoy wanda ya taba cewa "Rubuta dokoki na da sauki, amma jagoranci da su nada matukar wahala".