Coronavirus a Kenya: Abin da ya sa 'yan kasar ba su yarda akwai cutar ba

A jerin rahotanninmu na Wasiƙu daga Ƴan Jaridar Afirka, Waihiga Mwaura ya nemi sanin dalilan da ƴan Kenya masu yawa ba su ɗauki annobar korona da muhimmanci ba.

Duk da alƙaluman da ke nuna illar da cutar Covid-19 a sassan duniya, wadda kuma tayi sanadin mutuwar kusan mutum 600,000, idan ka bayyana cewa ka kamu da cutar a Kenya kana iya samun kanka cikin waɗanda al'umma ke ƙaryatawa ko wanda ke neman farin jini ko kuma dan koron gwamnati.

Wannan lamarin ya fara ne kan Ivy Brenda Rotich wadda ita ce ƴar Kenya da aka fara sallama daga asibiti a watan Afrilu bayan an yi ma ta magani bayan ta kamu da cutar korona.

Ms Rotich ta sha suka a shafukan sada zumunta, inda wasu ke cewa gwamnatin ƙasar ce ta ke amfani da ita domin ta gamsar da ƴan Kenya cewa cutar Covid-19 ba ƙarya ce ba, ko domin ƙasar ta ci gaba da samun tallafi daga ƙasashen waje domin yaƙi da cutar.

A wancan lokacin ana kallon cutar korona a matsayin ta ƴan ƙasashen waje ce kuma wai ƴan Afirka na ganin ba za ta iya kama su ba.

A halin yanzu da ƴan Kenya fiye da 11,000 suka kamu da cutar kuma wasu 200 cikinsu suka mutu, akwai waɗanda har yanzu ke cewa babu cutar - daga wani wanda ya wanke min motata a makon jiya, wanda ya kafe cewa labarin cutar babbar ƙarya ce, zuwa ƴan jarida da ke cewa cutar ba komai ba ce face wata mura mai wuyar warkarwa.

Akwai kuma wani sanannen fasto mai suna Robert Burale da wasu suka tuhuma da yin ƙaryar kamuwa da cutar duk da hotunan da suka nuna shi a wani asibitin Nairobi.

Akwai kuma shugaban ma'aikatar harkokin matasa Benson Musungu a gwamnatin tsohon firai minista Raila Odinga wanda shi ma aka ce ya karɓi wasu maƙudan kuɗaɗe daga gwamnati domin wai ya amsa cewa ya sami kulawa ta kwana 15 a sashen kulawa da masu cutar korona na wani asibitin wani gari.

Saboda haka masu cutar da dama sun gwammace yin shiru domin gudun cin zarafi daga jama'ar kasar.

'Ƴan siyasa ma ba sa taimakawa'

Ƴan siyasa da wasu shugabannin al'umma da ke da ƙarfin faɗa a ji ma na kamuwa da cutar korona amma sai suka zaɓi suyi shiru domin gudun a kyamace su.

Saboda haka ne mutanen da suka warke daga cutar ƙalilan ne ke sanar da jama'a halin da suka shiga, kuma a kan ci karo da tambaya kamar "Akwai waɗanda suka taba ganin wanda ya kamu da Covid-19?"

Yawancin waɗanda ke amsa tamabayar na cewa "A'a" ne.

A farkon watan Yuli wani ɗan majalisa Jude Njomo yayin da yake bayar da bahasi a gaban kwamitin da ke sa ido kan harkar kiwon lafiya a majalisar ƙasar, ya sanar cewa iyalinsa sun shiga cikin damuwa bayan da aka sanar da su cewa mahaifiyarsa tana da cutar kwana huɗu bayan ta mutu, kuma a sanadiyyar haka suka binne ta cikin dare cikin gaggawa.

Ya ce "Na roƙi a bani ƙarin lokaci, amma kamar yadda doka ta tanada, an kira ni da ƙarfe 3 na rana kuma muka binne ta da ƙarfe 8 na dare. Ban ji daɗin haka ba ganin cewa ta shafe shekara 82, wanda ya kamata a ce an yi bikin da ya dace da matsayinta," kamar yadda ya sanar wa tashar talabijin ta Citizen TV mai zaman kan ta.

Mista Njomo ya ce daga baya shi da iyalansa sun sa an gwada su har sau biyu, kuma sakamakon ya nuna babu wanda ke ɗauke da cutar cikin iyalan gidansa.

Kuma yayin da gwamnatin ƙasar ta fara sassauta kullen da aka ƙaƙaba wa yawancin al'umma, a fili yake cewa wasu ba su yarda cewa cutar ma na iya yin illa ba.

A madadin haka, sun zabi su amince da ƙarairayin da ke yawo a kasar kan cutar, wanda ke nuna wagegen giɓin da ke tsakanin gwamnati da jama'ar ƙasar.

Kamar yadda Farfesa Omu Anzala, wanda kwararren likitan ƙwayoyi masu yaɗuwa ne a Jami'ar Nairobi, a al'adance ƴan Afirka ba sa son bayyana wasu abubuwa kamar kamuwa da ciwo.

Za ka ga shugaban ƙasa guda na ficewa ƙasashen waje domin neman lafiya amma ba zai sanar wa ƴan kasar halin da yake ciki ba.

Farfesa Anzala ya yi imani cewa gazawar masu aiki a bangaren kiwon lafiya na cikin dalilan da suka sa ƴan ƙasar ke ƙaryata cutar.

Ya kuma ce abu ne muhimmi su ci gaba da sauraron halin da ƴan ƙasar ke ciki, kuma su riƙa zaɓar kalmomin da za su dace da su, kana su haska wa jama'a wurin da yayi mu su duhu.