Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Matar da ta dafa wa ‘ya’yanta duwatsu saboda talauci
'Yan kasar Kenya sun hada hannu wajen taimaka wa wata mata da mijinta ya rasu kuma aka dauko hoton bidiyonta tana dafa wa 'ya'yanta takwas duwatsu domin hilatar su, su dauka cewa abinci take dafawa har su yi barci.
Peninah Bahati Kitsao, wadda ke zaune a Mombasa, ta yi fatan cewa barci zai kwashe 'ya'yan nata a yayin da take dafa musu duwatsun.
Matar tana yin sana'ar wankau ne, sai dai yanzu ba ta iya fita domin karbar wankin mutane saboda dokar kulle da aka sanya sakamakon cutar korona.
Wata makwabciyarta, Prisca Momanyi, wadda ta yi matukar kaduwa game da batun ce ta jawo hankalin kafafen watsa labarai game da halin da matar take ciki.
Bayan hirar da gidan talbijin na NTV da ke Kenya ya yi da ita, matar ta samu tallafin kudi ta hanyar asusun bankin da Ms Momanyi ta bude mata, saboda Ms Kitsao ba ta iya karatu da rubutu ba.
Ms Momanyi, wadda ke zaune a gida mai daki biyu ba tare da ruwan famfo ko wutar lantarki ba, ta bayyana kaunar da aka nuna mata a matsayin "mu'ujiza".
Ta shaida wa shafin intanet na Tuko news cewa "Ban taba tsammanin 'yan Kenya za su nuna min irin wannan kauna ba inda suka rika kira na a wayar tarho daga kowanne yanki suna tambaya ta irin taimakon da nake so su yi mini."
Ta shaida wa NTV cewa 'ya'yan nata ba su jima da gane cewa so take ta yaudare su don su yi barci ba ta hanyar dafa musu duwatsu.
"Sun fara bayyana min cewa sun gano karya nake yi musu, amma babu yadda na iya domin babu abin da zan dafa."
NTV ya rawaito cewa daga bisani makwabtanta sun rika zuwa gidan suna tambayar ta halin da take ciki bayan sun ji kukan 'ya'yan nata.
Gwamnatin kasar ta kaddamar da shirin ciyar da marasa galihu a wani bangare na takaita tasirin cutar korona.
Sai dai har yanzu wannan tallafi bai isa ga Ms Kitsao ba, wadda mijinta ya rasu bara sakamakon harbe shi da wani gungun mutane ya yi.
Makwabtanta sun gode wa karamar hukumarsu da kuma kungiyar agaji ta Kenya Red Cross, wadanda su ma suka tallafa wa Ms Kitsao.
Hukumomi sun ce marasa galihu da dama da ke yankin su Ms Kitsao za su ci moriyar tallafin da gwamnati za ta yi musu.
Kamar sauran marasa galihun kasar Kenya, ita ma Ms Kitsao ta kwashe watan jiya tana neman kudi tun da gwamnati ta sanya matakan dakile yaduwar cutar korna, ciki har da haramta tafiye-tafiye a ciki da wajen manyan birane, a cewar wakilin BBC a Nairobi, Basillioh Mutahi.
Kamfanoni da dama sun daina aiki ko da yake wasu sun takaita yadda suke aikin, abin da ya sa ma'aikatan da suka dogara da kananan ayyuka suka rasa ayyukan yi.
Su ma masu kananan sana'o'i dokar ta shafe su.
Labarin mawuyacin halin da Ms Kitsao take ciki ya zo daidai lokacin da aka bayyana cewa ma'aikatar lafiyar kasar ta kashe makudan kudaden da Hukumar Lafiya ta Duniya ta tallafa wa Kenya don dakile cutar korona, inda ta sayo ganyen shayi da cincin da katin wayar salula ga ma'aikatanta.
Ba a bayyana adadin mutane da aka bai wa wadannan abubuwa ba, sai dai batun ya janyo kakkausar suka a shafukan sada zumunta saboda kashe irin wadannan makudan kudade yayin da 'yan kasar suke cikin fatara.
Kenya tana da jumullar mutum 535 da suka harbu da cutar korona, yayin da mutum 182 suka warke ya zuwa ranar Talata, 5 ga watan Mayu.