Yadda faɗa kan dutsen guga ya janyo ɓatan wani matashi
Yayin da ake bikin tunawa da mutanen da suka bata, kuma aka daina jin duriyar su, BBC ta yi hira da wata mata Martina Dauda, da ɗanta ya bar gida kusan shekara goma ke nan daga garin Yola a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda matsalar ta fi kamari.
Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta keɓe 30 ga watan Agustan kowace shekara domin tunawa da irin waɗannan mutanen.
A cewar wani rahoton kungiyar bayar da agajin gaggawa ta ''International Committee of Red Cross'', fiye da mutum dubu arba'in daga nahiyar Afirka sun bace, kuma rabin adadinsu 'yan arewa maso gabashin Najeriya ne.
Martina Dauda ta shaida wa BBC cewa ɗan nata mai suna Marcus ya samu saɓani ne da yayansa kan dutsen guga kuma faɗan da aka yi masa ne ya sa ya bar gida kuma har yanzu bai koma ba.
A cewarta ta shiga ɗimuwa bayan da wasu suka kawo mata labarin cewa Marcus ya mutu amma "na dangana da Allah kawai."
"Mun je gidan yari, mun tambaya kowa sai ya ce bai san inda yake ba, shi ke nan na bar wa Allah kawai." in ji ta.
Ta ce a lokacin da ya ɓata, Marcus yana da shekara 18 a duniya.








