Nathaniel Julius: An kama 'yan sanda a Afrika Ta Kudu kan harbe yaro mai shekara 16

/

Asalin hoton, AFP

An kama wasu 'yan sanda biyu a Afrika Ta Kudu sakamakon harbe wani yaro mai shekara 16 wanda kisan yaron ya jawo zanga-zanga a titunan ƙasar.

Iyayen Nathaniel Julius sun bayyana cewa sun tafi sawo wa yaron biscuit inda suka dawo suka tarar an harbe shi.

Rundunar 'yan sanda a ƙasar ta bayyana cewa za a tuhumi 'yan sandan da laifin aikata kisa.

Iyayen Julius sun bayyana cewa an harbe Julius sakamakon ya kasa amsa tambayoyin da 'yan sandan suka yi masa.

Sai dai sun bayyana cewa ya gaza amsa tambayoyin ne saboda irin naƙasar da Nathaniel ɗin yake tattare da ita.

Tun a farko 'yan sandan sun bayyana cewa an harbe Julius ne bisa kuskure a daidai lokacin da 'yan sandan ke bata kashi da wasu 'yan daba.

Sashen bincike na 'yan sanda mai zaman kansa a ƙasar ya bayyana cewa an yanke shawarar kama 'yan sandan bayan an yi bincike kan hujjojin da aka bayar.

Bayan mutuwar Julius a daren Laraba, ɗaruruwan mazauna yankin suka hau tituna domin gudanar da zanga-zanga a ranar Alhamis, wanda hakan ya sa aka samu arangama tsakanin 'yan sandan da masu zanga-zangar.

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ɗaruruwan mazauna yankin ne suka hau kan tituna domin gudanar da zanga-zanga
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, 'Yan sanda su harba harsasan roba domin korar masu zanga-zangar.

'Yan sandan sun yi amfani da harsasan roba da wasu makamai domin tarwatsa masu zanga-zangar waɗanda ke jifar 'yan sandan da duwatsu.

Masu zanga-zangar dai sun sa shingaye da ƙone-ƙone kan tituna domin nuna fushinsu.

Ana yawan zargin 'yan sanda a Afrika Ta Kudu da amfani da ƙarfin da ya wuce kima. An zargi jami'an tsaron ƙasar da kashe akalla mutum 10 a wannan shekara a yunƙurinsu na tursasa wa jama'ar ƙasar bin dokar da aka sa ta kulle kan cutar korona.

Kashe Nathaniel ya girgiza mutane da dama ba wai a Afrika Ta Kudu ba, har da wasu sassan duniya.

Kashe shi ya sosa wa wasu Amurkawa inda ke yi musu ƙaiƙayi, inda dama tuni suna zanga-zanga kan yadda 'yan sanda ke muzguna wa baƙar fata a ƙasar. Fitattun mutane da dama na Amurka sun tofa albarkacin bakinsu a shafin Twitter kan kisan Nathaniel.

Yankin da Nathaniel ya fito a Afrika Ta Kudu suna cikin ɓacin rai - abin da suke so a halin yanzu shi ne a ɗauki mataki kan wannan lamarin.

Sai dai akasari jama'ar ƙasar na kokawa da kotunan ƙasar sakamakon rashin adalcin da suke zargin ana yi musu,.

Ko sau nawa suka yi zanga-zanga kuma ko sau nawa kafafen yaɗa labarai na gida da na waje za su yi labari kan wani lamari ba shi zai sa kotuna a ƙasar ba su yi hukuncin da ya dace.