Coronavirus a Afirka Ta Kudu: Yadda sanyi ke kashe masu cutar korona da ake killace wa a tanti

South African Jeanette Mlombo, whose son Martin died last month at Sebokeng Hospital at the age of 30.
Bayanan hoto, Jeanette Mlombo ta ce cin hanci da rashin kula ne ya jawo mutuwar ɗanta
    • Marubuci, Daga Andrew Harding
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Sebokeng

Ana shafe watanni ba a tuna da waɗanda ake tunanin suna ɗauke da cutar korona ba a inda aka ajiye a buɗe, wuri kuma mai sanyi a wajen asibitin Afirka Ta Kudu tsakiyar hunturu lokacin da ake fama da yaɗuwar korona wanda ya kai ga mutuwar masu fama da cuta da "dama" suna ƙanƙare, kamar yadda wani bincike na musamman na BBC ya nuna.

An bankaɗo wannan ne yayin da gwamnatin Afirka Ta Kudu ta amsa da kuma yin Allah-wadai da rashawa da almundahana suka yi katutu a yaƙin da ƙasar ke yi da korona.

"Akwai bala'in sanyi a cikin tantin. Da zarar dare ya yi ba sauƙi, za ka iya ganin yadda masu cutar ke raguwa. Kuma matsalar ɗaukewar zafin jiki ta Hypothermia ne ke kashe mutune musamman a cikin tanti," kamar yadda wani likita a asibitin Sebokeng - wanda ya kwarmata wa BBC kuma aka ɓoye sunansa.

Likitan ya ce mutum 14 aka bayar da rahotannin sun mutu a cikin tanti tsawon sa'a 48 - kuma ba duka cutar Hypothermia ba ce.

'Rashin tsari'

"Mun gaji kuma cike da fushi da fargaba kan majinyatanmu, na tambayi kaina mutum nawa za su iya mutuwa haka kawai kafin kaddamar da bincike."

Medics in a tent at Sebokeng Hospital, South Africa
Bayanan hoto, Wajen ajiye motoci aka gyara aka yi wa tanti ana killace mutane a asibitin Sebokeng

Likitan ya bayyana abubuwan da ya gani masu ban tsoro a inda ake killace mutane - wurin ajiye motoci da asibitin ta mayar wurin sauraren marar lafiya - cikin yanayin matsanancin sanyi a makwannin Yuli, inda masu manyan shekaru ke faɗuwa bayan watsi da shi tsawon kwana biyu ko fiye da haka ba tare da kula da shi ba ta fuskar tsabta da abinci da ɗumamawa.

Ta ce ana tilastawa marar lafiya haɗa taro gaban wasu ƙananan na'urorin ɗumama ɗaki da suke yawan lalacewa.

"Ina jin takaci, da rashin tabbas. Rashin kayayyaki a wurin killace jama'a wani abin wasa ne...

"Ba mu da magunguna. Ba abin taimakawa numfashi. An jefar da rigunan kariya ta ko ina da ka iya yaɗa cutar ga wasu mutanen,'' in ji likitan, wanda ya yi ƙorafi cewa ma'aiakatan jinya da dama sun kamu da cutar sakamakon rashin kyawun yanayin.

"Cin hanci ne kawai da rashin kula," a cewar Jeanette Mlombo, wadda ɗanta Martin ya mutu a watan da ya gabata a asbitin Sebokeng, yana da shekara 30.

Ta ce ba a yi masa gwajin Covid-19 ba kuma tun farko ya fara kukan kumburin ƙafa ne, amma aka bar shi tsawon sa'a 12 a cikin tantin.

''Yana jin tsananin sanyi. Yana karkarwa, kuma jin yunwa. Ya ce: 'Haka na shafe dare babu abin rufa. Zan mutu. Babu mai kula da ni,'' kamar yadda Ms Mlombo ta faɗa.

2px presentational grey line

Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:

2px presentational grey line

Wasu saƙonni da suka ɓulla sun nuna cewa matakin amfani da tantin ya harzuƙa ƙwararru a ɓangaren lafiya.

Wata tataunawa da aka yi ta cikin gida a dandalin Whatsapp da BBC ta gani, ta nuna yadda masana harkar lafiya suka dinga bai wa gwamnati shawarar cewa kar a yi amfani da tantuna, saboda gudun sanya marasa lafiya cikin hadari.

Screengrab of WhatsApp messages exchanged by medics at Sebokeng Hospital

Daga cikin tattaunawar akwai:

  • "Tantuna na da sanyi a yanzu."
  • "Ban taɓa goyon bayan a yi tantuna ba... Ina ganin barin mutane su kwana a tauntunan zalinci ne.''
  • "Ban taɓa yarda da batun tantuna ba."

Akwai kayan aiki a asibiti

Da yake mayar da martani kan zarge-zargen bankaɗar kan Asibitin Sebokeng Hospital, wani mai magana da yawun ɓangaren Lafiya na Gauteng ya yi watsi da batun cewa mutane da dama sun mutu saboda sanyi, inda ya rubuta email cewa ƙiyasin da aka yi duba da rahoton asibitin bai haɗa da mace-macen da aka samu sakamakon sanyin da jikin mutum kan yi.

Ya kuma yi watsi da zarge-zargen cewa babu isassun rigunan kariya da sauran kayan amfanin asibiti.

Yanayin ya inganta a makonni da suka gabata a asibitin Sebokeng, saboda matakan da hukumar asibitin ta ɗauka da kuma yadda yawan masu kamuwa da cutar suka ragu.

Bundles of South African rand notes showing the face of Nelson Mandela placed behind a vial of blood laballed coroanvirus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Farashin takunkumi ya hau da kashi 900 a Afrika Ta Kudu a lokacin annobar