Coronavirus a Kenya: Annobar korona ta sa makarantu sun koma wurin kiwon kaji

Matakin da ƙasar Kenya ta ɗauka na rufe makarantu har zuwa watan Janairu saboda annobar korona ya sanya makarantu masu zaman kansu cikin mawuyacin hali, kamar yadda Basillioh Mutahi da Mercy Juma suka rawaito.
Azuzuwan makarantar Mwea Brethren, wadda a baya take kaurewa da sowar ɗalibai, yanzu cike suke da sowar kaji.
A kan allon bango, an maye gurbin tambaya da amsar ilimin lissafi da jadawalin yi wa kaji allurar riga-kafi.
Joseph Maina, mai makarantar, ya gwammace ya koma kiwon dabbobin domin samun kuɗi saboda an daina samun kuɗin daga ɓangaren koyarwa.
'Abubuwan da za su taimaka a tsira'
Rayuwa ta fi ƙuntata a watan Maris a lokacin da aka umarci dukkanin makarantu su rufe, yayin da yake tsaka da biyan bashi, abin da ya sa dole ya sake ƙulla yarjejeniya da banki.
Da farko kamar komai ya ɓalɓalce, amma "mun yanke shawarar cewa lallai sai mun yi wani abu domin mu tsira da rayuwarmu," Mista Maina ya shaida wa BBC.

Makarantu ƙalilan ne suka iya ci gaba da koyar da ɗalibai ta intanet amma kuɗin da suke samu ba ya iya biyan buƙatun malaman, a cewar ƙungiyar Kenya Private Schools Association (KPSA) ta makarantu masu zaman kansu.
Kusan kashi 95 cikikn 100 na ma'aikata 300,000 na makarantu masu zaman kansu aka daina bai wa albashi, in ji Peter Ndoro, shugaban ƙungiyar KPSA.
Bugu da ƙari, an umarci makaranta 133 su kulle har sai baba ta gani.

Domin guje wa ɗaukar mummunan mataki, wata makaranta mai suna Roka Preparatory ita ma ta mayar da filin makarantar gona.
"Abubuwa ba su lalacewa kamar yanzu ba," in ji James Kung'u, wanda ya kafa makarantar shekara 23 da suka wuce, a hirarsa da BBC.

Shi ma kuma yana kiwon kaji.
"Yanayin da na shiga irin na sauran makarantun ne. Ina fama kafin na iya sayen man fetur a motata. Babu ɗalibai babu malamai yanzu. Wannan abu ya shafi tunaninmu ƙwarai da gaske," a cewar Kung'u.
Babu aikin yi ga malamai
Bayan makarantun biyu sun samu wata hanyar samun kuɗi ta daban, masu makarantun na cikin damuwa game da halin da ma'aikatansu za su shiga, waɗanda suka shafe wata biyar ba tare da albashi ba.
Sai dai malaman makarantun gwamnati sun ci gaba da karɓar albashinsu.

A madadin haka, da dama daga cikinsu sun sauya sana'a.
Macrine Otieno - wadda ta shafe shekara shida tana koyarwa a wata makaranta - an kore ta daga gidan da take zaune saboda ta kasa biyan kuɗin haya.
Ta zama mai rainon yara domin ta riƙa samun abinci da wurin kwana.
"Tun sanda aka samu mutum na farko da ya kamu da korona a Kenya kuma aka rufe makarantu, babu wani da nake yi.
"Na yi ƙaoƙari na samu abin da zan yi don ciyar da yarona amma abin ba sauƙi," in ji ta.













