Alassane Ouattara: Tashin hankali ya barke a Ivory Coast bayan tsayar da shugaban kasa takara karo na uku

Bayanan da ke fitowa daga Ivory Coast na cewa tashin hankali ya barke a sassan kasar bayan da jam'iyya mai mulkin kasar ta zabi Shugaba Alassane Ouattara ya tsaya takara a karo na uku a zaben watan Oktoba.

Magoya bayan jam'iyyun adawa da na shugaban kasar sun kara a birnin Divo da ke kudancin kasar inda aka cinna wa wasu gine-gine wuta.

An kuma kona tayoyin mota da kafa shingaye a Gagnoa, wanda shi ne asalin garin tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo.

A farkon wannan shekarar Mista Ouattara ya ce ba zai sake tsayawa takara ba. Amma ya sauya ra'ayi bayan da mutumin da ya so ya gaje shi - wato Firaiminista Amadou Gon Coulibaly ya yi mutuwar fuju'a a watan Yuli.

Yayin da yake magana a wani gangamin siyasa a Abidjan, Mista Ouattara ya ce sauyin da aka yi wa tsarin mulkin kasar a 2016 (wanda ya hana duk wani shugaban da ya yi mulki sau biyu ya sake neman wa'adi na uku), an yi shi ne domin ci gaban Ivory Coast:

"An yi wannan tsarin mulkin domin kare muradin Ivory Coast ne. Na yi shi ne domin 'yan kasar, na yi shi ne domin mu kaucewa fadawa cikin hatsari - irin wanda ke haifar da juyin mulki da wanda ke neman sanin asalin iyayen ko kakannin dan takara kafin a bar shi ya tsaya takara."

Ya kara da cewa, "Na so in kaucewa irin wadannan muhawarorin da suka yi wa Ivory Coast mummunar illa."

Sauya ra'ayin da Mista Ouattara ya yi ya bata wa magoya bayan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo wanda aka hambare daga mulki domin neman makale wa kan karagar mulki.

Ayar tambaya a nan ita ce: shin da wace hujja Mista Ouattara ke son tsawaita nasa mulkin bayan barnar da irin wannan halayyara ta haifar a baya - lamarin da ka iya mayar da kasar cikin yakin basasa?