Amadou Gon Coulibaly: Yadda Firaministan Ivory Coast ya yi mutuwar fuju'a a taron ministoci

Firaministan Ivory Coast Amadou Gon Coulibaly ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya a wajen taron majalisar ministocin ƙasar..

Shugaban ƙasar Alassane Ouattara ne ya tabbatar da hakan inda ya ce marigayin ya fara rashin lafiyar ne lokacin da ake tsakiyar taron majalisar zartarwa, kuma daga nan ne aka kai shi asibiti inda ya rasu a can.

Shugaba Alassane Ouattara ya ce al'ummar ƙasar na cikin makoki.

Kafin rasuwarsa, Mista Coulibaly ne aka sa ran cewa zai tsaya takarar shugabancin ƙasar ƙarƙashin jam'iyyar RDR mai mulki a watan Oktoba.

Marigayin kuma ya rasu ne mako guda bayan ya dawo daga ƙasar Faransa inda ya shafe wata biyu yana jinya sakamakon matsalar da ta danganci ciwon zuciya.

Ya kuma shafe shekara uku kan kujerarsa ta Fira minista.

Rasuwar Amadou Gon Coulibaly ta janyo wani gagarumin rashin tabbas kan zaɓen ƙasar, wanda Shugaba Alassane Ouattara ya ce ba zai sake tsayawa takara ba.

Tuni dai Shugaba Alassane Ouattara ya bayyana ta'aziyya bayan mutuwar fuju'a da fira minista kuma ɗan takarar shugabancin ƙasar, Amadou Gon Coulibaly ya yi.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya karanta ta talbijin, Shugaba Alassane Outtara ya ce mutuwar ta dugunzuma shi.

"Ya 'yan uwa al'ummar ƙasa, Ivory Coast tana makoki. Cikin tsananin raɗaɗi nake sanar da ku cewa fira minista Amadou Gon Coulibaly, shugaban gwamnati ya bar mu da farko-farkon yammaci bayan halartar taron Majalisar zartarwa ranar Laraba 8 ga watan Yuli a fadar shugaban ƙasa.

Zan so a madadin gwamnati da madadin ni kaina, na miƙa zuzzurfar ta'aziyya ga iyalin Gon Coulibaly da ɗaukacin makusantansa da ma illahirin al'ummar Ivory Coast, in ji shi.

"Ina taya juyayi ga ƙanina kuma ɗana, Amadou Gon Coulibaly, wanda tsawon shekara talatin ya kasance babban aminina.

Cikin jimami ina sarawa ɗan ƙasa nagari mai matuƙar biyayya da sadaukarwa da nuna ƙauna ga ƙasarmu. Ya tattara ɗabi'un zuri'a mai tasowa ta jami'an Ivory Coast da ke da matuƙar ƙwarewa da tsananin biyayya ga ƙasa<" cewar Shugaba Ouattara.