Coronavirus a Najeriya: Yadda za ku yi zaɓe lokacin cutar korona

Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar zaben Najeriya za ta gudanar da zabe a karon farko tun bayan bullar cutar korona a kasar.

Hukumar za ta yi zaben cike gurbi ne na dan majalisar dokoki a jihar Nasarawa a ranar asabar 8 ga watan Yuli.

Nick Dazang shi ne daraktan watsa labarai da wayar da kai na hukumar zaben, ya kuma bayyanawa BBC sabbin sharuɗan da annobar korona ta sa su gindayawa lokacin zaben.

Amma ya ce gabanin duka wadannan matakai sai da hukumar ta tattauna da masu ruwa da tsaki domin ganin shirin nasu ya tafi yadda aka tsara su.

Za a bude rumfunan zabe 8:30 sannan a tabbatar an ja layi yadda mutane ya kamata su ba da tazara tsakaninsu, domin gudun yaɗa wannan cuta tsakanin masu zabe.

Dole ko wanne mai kaɗa kuria ya sanya takunkumi yayin jefa kuri'arsa, duk wanda kuma ya je wurin zabe ba tare da wannan takunkumi ba za a sa jami'ai su yi waje da shi daga filin zaben.

Sanya takunkumin in ji Nick zai zama wata kariya ga wadanda suke filin zaben da kuma wanda ya sanya shi. Don haka ba zabi ba ne ga masu kaɗa zabe.

Za a jibge iya mai'an 'yan sanda 500 a wurin zaben domin kiyaye rikici irin na siyasa, kuma Nick ya ce da yiwuwar samun karin jami'an tsaro daga wasu wuraren.

INEC din ta kuma wallafa a shafint na Twitter wani sako kan yadda mutane za su iya bibiyar zaben daga inda suke.

Wannan sabon ci gaba da aka samu a iya cewa ya zo daidai lokacin da ake bukatarsa domin rage turmutsutsun mutane yayin zabe.

Sai dai ita INEC ta ce ta samar da wannan ci gaba ne domin tabbatar da an yi komai a bude babu muna-muna.

Akwai zaben gwamnan jihar Edo da za a yi a watan Satumba shi ne zabe na gaba da ake sa ran za a yi a kasar cikin wannan yanayi na korona.