Tottenham na zawarcin Diaz, Beckham na son ɗauko Suarez

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Tottenham Hotspur Jose Mourinho yana son dauko dan wasan Colombia Luis Diaz, mai shekara 23, daga Porto.(Record - in Portuguese)
Inter Miami, kungiyar da tsohon kyaftin na Ingila David Beckham ya mallaka, tana son dan wasan Barcelona da Uruguay Luis Suarez, mai shekara 33. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Wakilin David Alaba, dan wasan da Manchester City da kuma Paris St-Germain suke zawarci ya nemi Bayern Munich ta rika biyan dan wasan mai shekara 28 dan kasar Austria euro 20m duk shekara domin ya tsawaita zamansa. (Bild - in German)
Tattaunawa tsakanin Manchester United da golanta mai shekara 23 Dean Henderson - wanda ya kwashe kakar wasan bana yana zaman aro a Sheffield United - ta shiga mataki mai muhimmanci bayan sun shafe makonni suna yin sulhu. (Sky Sports)
Chelsea ta bayar da fifiko wajen dauko dan wasan Leicester City dan kasar Ingila Ben Chilwell, mai shekara 23, a kan sauran 'yan wasan irinsu dan wasan Ajax dan kasar Argentina Nicholas Tagliafico, 27, da kuma dan wasan Getafe dan kasar Sufaniya Marc Cucurella, mai shekara 22. (Goal)
West Ham United na sha'awar dauko dan wasan Queens Park Rangers kuma tsohon wanda ke buga gasar 'yan kasa da shekara 21 a Jamhuriyar Ireland Ryan Manning, mai shekara 24. (Telegraph - subscription required).
Atletico Madrid ta ki amincewa da sabon tayin euro 25m da Arsenal ta yi da kuma ba ta dan wasan Faransa Matteo Guendouzi, don sayen dan wasan Ghana Thomas Partey, mai shekara 27. (AS - in Spanish)
Tsohon golan Burnley, West Ham da kuma Manchester City Joe Hart, mai shekara 33, yana dab da tafiya Celtic.(Sun)
Dan wasan Brazil Hulk, mai shekara 34, yana duba yiwuwar tafiya kungiyar da ke buga Premier League idan kwangilarsa a kare a Shanghai SIPG a watan Janairu. (Talksport)
Leeds United tana son dauko dan wasan FC Utrecht dan shekara 2 Sean Klaiber a yayin da take son shiga kasuwar musayar 'yan kwallo da wuri. (Voetbal International - in Dutch)
Sai dai burinLeeds na dauko dan wasanArgentina Thiago Almada yana busashewa, a yayin da dan wasan mai shekara 19 ya gaya wa abokan wasansa a kungiyar Velez Sarsfield cewa yana so ya ci gaba da zama a kasarsa. (Leeds Live)
Barcelona tana son sayar da dan wasan da ta saya a watan Fabrairu Martin Braithwaite, mai shekara 29, saboda dan wasan na Denmark ba ya cikin tsarin kocin kungiyar Quique Setien na kakar wasa mai zuwa. (Mundo Deportivo - in Spanish)











