Manchester City na neman Torres, Tottenham na zawarcin Hojbjerg

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City tana son dauko dan wasan Valencia dan kasar Sufaniya Ferran Torres, mai shekara 20, idan aka soma musayar 'yan kwallo a kakar wasan bana. (ESPN)
Tottenham na dab da dauko dan wasan tsakiyar Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24, daga Southampton. (Sky Sports)
Arsenal, Tottenham da kuma Leicester suna son karbo dan wasan Barcelona da Brazil Philipe Coutinho, mai shekara 28, wanda yanzu haka yake zaman aro a Bayern Munich. (Sport - in Spanish)
Shugaban Atletico Madrid Enrique Cerezo ya yi watsi da rade radin da ake yi cewa golan Slovenia Jan Oblak, mai shekara 27, zai bar kungiyar. (Marca - in Spanish)
West Ham ta kara kaimi a yunkurinta na dauko dan wasan QPR mai shekara 22, Eberechi Eze, wanda farashinsa ya kai £20m. (Guardian)
Leeds United ta ware £15m domin dauko dan wasan Tottenham da Argentina Juan Foyth, 22. (Sun)
Har yanzu Roma ba ta kulla yarjejeniya ba da Manchester United a kan sayen dan wasan Ingila Chris Smalling, mai shekara 30. (Corriere dello Sport - in Italian)
Lazio tana tattaunawa da dan wasan Manchester City dan kasar Sufaniya David Silva, mai shekara 34. (AS)
Dan wasan Chelsea da Brazil Willian, mai shekara 31, wanda kwangilarsa za ta kare a bazara, ya samu gayyata "mai kwari" daga wasu kungiyoyin Premier League, a cewar wakilinsa. (Talksport)
Wanda yake son sayen Sunderland ya yi alkawarin ware £50m don dauko 'yan wasan Premier League. (Sun)
Everton tana son dauko dan wasan Serbia kuma tsohon dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic, mai shekara 36, daga Zenit Saint Petersburg. (Vecernjih Novosti - in Serbian)
Real Madrid tana sanya ido kan dan wasan Sevilla dan kasar Faransa mai shekara 21 Jules Kounde. (ESPN)











