Mariano: Dan kwallon Real Madrid ya kamu da korona

Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon Real Madrid Mariano ya kamu da cutar korona, kamar yadda kulob din ya bayyana.
Sanarwar da kungiyar ta fitar, ta ce dan wasan mai shekaru 26 na cikin koshin lafiya kuma a yanzu haka yana can ya killace kansa a gida.
Bai buga wasan da Real ta tashi biyu da biyu a wasa tsakaninta da Leganes a ranar 19 ga watan Yuli.
Madrid za ta fuskanci Manchester City a zagaye na biyu na gasar zakarun Turai a ranar 7 ga watan Agusta.
Mariano ya buga wasanni bakwai a bana tare da Real Madrid a shekara ta 2020 kuma ya zura kwallo a wasan da suka doke Barcelona a watan Maris abin da ya taimaka wa Real Madrid a matsayin zakarun kasar Spaniya.







