Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Facebook: 'Yadda masu kutsen intanet suka galabaita ni'
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau
Manyan attajiran duniya irinsu Jeff Bezos da Bill Gates da Elon Musk sun wayi gari da mummunan labarin yin kutse a shafukansu na sada zumunta musamman Twitter a ranar Laraba.
Ba attajirai kaɗai ba, har da taurari irinsu Kanye West da matarsa Kim Kardashian, da 'yan siyasa irinsu Barack Obama - tsohon shugaban Amurika.
An wallafa saƙwannin jabu a shafukan mutanen da kutsen ya shafa, inda aka buƙaci mutane su aika gudunmawar dala 1,000 na kuɗin bitcoin da fatan samun ribar ninkin kuɗin.
An daɗe ana yi wa ɗaiɗaikun mutane kutse a shafukansu ba musamman a Facebook.
Mutane da dama sun wayi gari da wani suna na daban a kan shafukansu da kuma hotuna tare da tura wa abokansu saƙwanni na cutarwa da sunansu bayan masu kutse a intanet sun ƙwace iko da shafukan nasu.
BBC ta samu jin labarin mutum biyu da irin hakan ta faru da su.
Sai da na kai rahoto wurin 'yan sanda - Ismail Mudi Hamza
Bayan masu kutsen sun ƙwace iko da shafinsa na Facebook, sai suka fara tura wa abokansa buƙatar neman kuɗi da zummar harkar kasuwanci da ka iya ba su riba - kamar dai yadda aka yi wa waɗancan manyan attajiran.
Ismail Mudi ya yi yunƙurin shiga shafin nasa Facebook amma abu ya gagara.
"Kawai sai abokaina na kusa suka fara kirana suna tambaya; 'wai me abin da ka turo mana yake nufi ne?," in ji Ismail.
A lokacin ne Ismail ya tabbatar cewa akwai matsala mai girma, domin kuwa duk abin da suka riƙa tura wa abokan nasa an yi shi ne da sunansa kuma bai ma san me aka tura ba.
"Sun riƙa tura wa mutane cewa ai ni ma na shiga harkar kuma har ma na samu ribar naira 100,000."
Bai yi wata-wata ba ya buɗe sabon shafi sannan ya wallafa bayanin yana mai sanar da abokansa cewa ba fa shi ba ne yake tura musu waɗannan bayanai ba.
"A ƙarshe dai wurin 'yan sanda na je na kai rahoto, su ma suka ce mani hakan ta faru da wasu da yawa. Suka ba ni takarda suka ce na ajiye kwafi, su ma za su ajiye kwafi.
"An yi ta ƙoƙari domin a ƙwato mani shafina daga hannunsu (masu kutse) amma abin ya ci tura."
Ismail ya ce ba a iya ƙwato masa shafinsa na asali ba daga hannun masu "garkuwar", sai wani sabo ya buɗe, in da aka tilasta masa sauya suna daga Esmael Mahmoud zuwa Ismail Mudi Hamza.
Ya ƙara da cewa sun wahalar da shi musamman ganin yadda har bayan ya buɗe sabo amma abokansa na kiransa domin neman ƙarin bayani.
Sun sauya mani suna, sun goge hotunana baki ɗaya - Bashir Adamu
Shi ma Bashir Adamu Facebook ɗinsa aka yi garkuwa da shi amma labarinsa ya ɗan sha bamban da na Ismail.
"Haka kawai na wayi gari na ga an sauya mani suna a shafina," in ji Bashir yana mai matuƙar mamaki.
An sauya masa suna daga Bashir Adamu zuwa Anberw.
Ya ce ba iya haka suka tsaya ba, sun kuma goge masa hotunansa baki ɗaya, kodayake Allah ya taimake shi ba su saka wasu daban ba.