'An saci bayanan mutane miliyan 50 a Facebook'

Kamfanin Facebook ya ce ya gano wasu matsaloli na tsaro da suka shafi kusan mutane miliyan hamsin na masu mu'amula da shi.

Kamfanin ya ce masu kutse sun yi nasarar kai wa ga wani maballinsa da zai ba su damar kai wa ga satar bayanan mutane.

Kamfanin na Facebook ya ce duk da ya kaddamar da bincike amma har yanzu bai kai ga gano wadanda suka yi kutsen ba.

Hukumar da ke sa ido ga kutsen intanet ta yi gargadi ga masu amfani da shafin facebook da su yi taka tsantsan bayan matsalar tsaro da aka gano ta shafi masu amfani da shafin kusan miliyan 50.

Tun a ranar talata ne Facebook ya gano an masa kutse, amma kuma sai a ranar juma'a ne shugabannin kamfanin suka sanar da matsalar ga masu amfani da shafin.

Kuma Shugaban kamfanin na facebook Mark Zuckerberg ya ce suna kan bincike domin gano girman matsalar.

''Ya ce abin da muka sani a yanzu shi ne masu kutsen sun bi hanyoyi ne na samun wasu bayanai na mutane da suka shafi suna da jinsi da kuma garin mutum kuma suna iya amfani da shafin mutum tamkar nasu ne, amma mun kaddamar da bincike domin gano girman matsalar."

Facebook dai nada yawan masu amfani da shafin sama da biliyan biyu a duniya, kuma zuwa yanzu ba a bayyana mutane ko kasashen da matsalar ta shafa ba.

A baya facebook ya fuskanci irin wannan matsalar ta tatsar bayanan miliyoyin mutane da ake zargin wani kamfanin sadarwa ya yi da ake kira Cambridge Analytica.