Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Elon Musk, Obama da Bill Gates na cikin fitattun mutane da aka yi wa kutse a shafin Twitter
An yi wa shafukan tiwita na manyan mutane da kamfanoni ciki har da Barack Obama da Bill Gates kutse, a wani al'amari wanda ga alama shiryayyen hari ne mafi girma ga dandalin sada zumuntar.
Ɗan takarar shugaban Amurka na jam'iyyar Dimokrat, Joe Biden na cikin mutanen da kutsen ya shafa, da kamfanin Apple da Uber da fitaccen mawaƙi Kanye West da Jeff Bezos.
A wani ɓangare na zambar, an wallafa saƙwannin jabu a shafukan mutanen da kutsen ya shafa, inda aka buƙaci mutane su aika gudunmawar dala dubu ɗaya na kuɗin bitcoin, da fatan samun ninkin kuɗinsu.
Asusun bitcoin ya samu kuɗi fiye da dala dubu ɗari zuwa yanzu.
Wani babban editan wata kafar yaɗa labaran harkokin fasaha a intanet, da ake kira CNET, Dan Ackerman ya ce salon damfarar yana kama da na masu aikon imel.
"Wannan kusan wani salon zamani ne saƙwannin imel ɗin damfara da kuka saba samu, inda ake tambayar mutum ya aika wa wani wasu 'yan kuɗaɗe don su fitar da wasu maƙudan kuɗi ta hanyar cekin banki da za a aiko musu da rabin kuɗin idan an cire.
Ya ce kowanne mashahurin mutum da irin yadda nasa saƙon ya bambanta, wasu an aika musu cewa 'Zan ɗan yi wa jama'a abin alheri, aiko min wasu kuɗin bitcoin a wannan adireshi maras suna, ni kuma zan mayar maka da ninkin duk abin da ka turo min".
Dan ya ce a zahiri za a ji tamkar wata raha ce amma idan saƙon ya fito daga ingantaccen shafin sada zumunta, kuma daga mutane sanannu, waɗanda aka san haƙiƙanin shafinsu ne, to mutane ƙarara suna iya faɗa wa wannan tarko.
Jerin wadanda aka yi wa kutse:
- Mawaki Kanye West
- Matarsa Kim Kardashian
- Tsohon shugaban Amurka Obama
- Ɗan takarar shugaban Amurka na jam'iyyar Dimokrat, Joe Biden
- Biloniya Mike Bloomberg
- Manhajar Uber
- Kamafanin Apple da ke kera wayar iPhone