Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda matsafa ke kutse a 'makabartun Kano'
Al'ummar yankin Rimin Kebe da ke jihar Kano a Najeriya sun koka kan abin da suka kira kutse da wasu batagari da suke yi wa kallon masu tsafi suke yi a makabartarsu da nufin aikata miyagun abubuwan da ba su dace ba.
Al'ummar yankin sun ce a lokuta da dama miyagun mutanen suna shiga cikin makabartar cikin dare domin aikata wasu abubuwa da ke da nasaba da tsafe-tsafe.
Sakataren masu kula da makabartar, Abdullahi Yusuf ya shaida wa BBC irin tashin hankalin da suke ciki a duk lokacin da suka yi ido biyu da tarkacen kayan tsafi da miyagun mutanen ke ajiyewa a cikin makabartar a lokacin da kafa ta dauke.
Yusuf ya ce makabartar ba ta da Katanga abin da ya ce ya ba da kofar wannan aika-aikar ta ci gaba.
Ya ce: ''A satin farko mun tsinci kwarya a cikin kabari rufe da ganyayyaki da allurai sun fi dubu a cikin kwaryar, a sati na biyu ma abin da muka gani kenan, a mako na uku kuwa koko muka gani na tukunya a lullube da likkafani an rubuta sunaye a jikinsa sai a mako na hudu kuma mun ga mukamukinsa a jiki an nannade da likkafani a kan kabarin jinjiri.' in ji Yusuf.
Abdullahi Yusuf ya ce kokarin da suke yi na ganin sun kawo karshen wannan abu ya ci tura saboda mutanen da ya kira masu neman duniya na shammatarsu ne yana mai kira ga gwamnatin jihar ta Kano da ta kai musu dauki.
Gwamnatin jihar Kanon ta bakin mai magana da yawun kwamitin kula da makabartu a jihar, Yusuf Tarauni ta ce za ta hukunta mutanen da ake zargi da yin aika-aikar domin zama darasi ga masu irin wannan dabi'a.
Ya ce daga cikin matakan da gwamnati za ta dauka domin dakile wannan matsala shi ne katange makabartar tare da samar da masu gadi da za su tabbatar da tsaron wajen.
Ya kuma yi kira ga jama'a da su tallafawa kokarin gwamnati ta hanyar ba da tasu gudummawar wajen samar da tsaro a wuraren da kai rahoton wanda ba a yadda da take-takensa ba ga hukuma.