Tolulope Arotile: Ƴar Najeriya da ta fara tuƙa helikwaftan yaƙi ta mutu

Matukiyar jirgin sama Tolulope Arotile

Asalin hoton, @hqnigerianairforce

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta sanar da mutuwar matukiyar jirgin sama Tolulope Arotile sakamakon hatsarin mota a Kaduna.

Sanarwar da kakakin rundunar Ibikunle Daramola ya fitar ta ce Arotile ita ce mace ta farko da ta fara tuka helikwaftan yaƙi a Najeriya wacce aka kaddamar a watan Satumban 2017.

Sanarwar ta ce matukiyar ta rasu ne a ranar Talata bayan gamuwa da hatsarin mota inda ta samu munanan raunika a Kaduna.

Marigayiyar wace ƴar asalin jihar Kogi ce, an bayyana cewa ta bayar da gudunmuwa sosai a yaki da ƴan bindiga masu fashin daji a jihar Neja inda ita ce ke tuka jiragen rundunar Gama Aiki.

Babban hafsan sojin sama na Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar ya ce mutuwar jami'ar babban rashi ga rundunar tare da jajantawa iyalanta a madadin dukkanin jami'an rundunar sojin sama na Najeriya.

Matukiyar jirgin sama Tolulope Arotile

Asalin hoton, @hqnigerianairforce

Matukiyar jirgin sama Tolulope Arotile

Asalin hoton, @hqnigerianairforce

Matukiyar jirgin sama Tolulope Arotile

Asalin hoton, @hqnigerianairforce

Matukiyar jirgin sama Tolulope Arotile

Asalin hoton, @hqnigerianairforce

Matukiyar jirgin sama Tolulope Arotile

Asalin hoton, @hqnigerianairforce