Abin da ya sa yake da kyau a koyi sabon harshe kafin a wuce shekara 20 da haihuwa

    • Marubuci, Daga Sophie Hardach
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future

Gari ya waye, kuma ana ta hada-hada a wata makarantar koyon harshen Sfaniyanci da ke arewacin Landan.

Iyaye na taimaka wa ƴaƴansu cire rigunansu na sanyi da hulunansu na kwano. Malamai kuma na tarbar yaran da kalaman "Buenos dias!"

A filin wasa, wata ƙaramar yarinya ta nemi a daure gashin kanta, irin ɗaurin da ake kira "coleta" (da sfaniyanci ana nufin daure gashi ya yi kama da bindin alade).

"A lokacin da yara ke ƙanana, ba koyon harsuna suke yi ba - mallakarsu suke yi," in ji shugaban makarantar Carmen Rampersad.

Wata kila shi ya sa waɗannan ƙananan yaran da ke makarantarta ke naɗar harsuna babu wata matsala.

Ga yawancin yaran Sfaniyanci shi ne yare na uku ko ma na huɗu da suka iya. Harshensu na ainihi na iya zama cCoatian, ko Hebrew ko Korean ko ma Dutch.

Idan aka kwatanta da yadda waɗanda suka girma ke kokawa wajen koyaon harsuna, sai ka iya cewa ya fi sauki mutum ya fara koyon harshe tun yana karami.

Amma kimiyya na da wani haske kan batun - kuma waɗanda suka girma za su so jin wannan labarin.

A takaice, kowa kan sami damar koyon harsuna amma ya danganta ga shekarunsa na haihuwa.

Yayin da muke jarirai, mun fi gane sautuka daban-daban; bayan mun zama yara kuma mun fi gane bambanci tsakanin yadda ake faɗin wasu kalmomi na yaren da suke koyo.

Manya kuma sun fi natsuwa da kwarewa wajen koyon sababbin abubuwa kamar koyon rubutu da karatu.

Wasa kwakwalwa na da alfanu

"Ba komai ne ke raguwa ba a lokacin da shekarun mutum ke karuwa", inji Antonella Sorace, malamin jami'a kan kwarewa wajen koyon harsuna, kuma shugaban wata cibiya da ke Jami'ar Edinburgh.

Masu bincike a kasar Isra'ila sun gano cewa manyan mutane sun fi gane tsarin harsuna.

Masanan sun raba mutane zuwa gida uku: Na farko sherunsu takwas, na biyu shekarunsu 12, na uku kuma matasa ne. sakamakon binciken ya nuna cewa manyan sun doke kananan yaran, inda masu shekara 12 kuma suka doke kannensu masu shekara takwas.

Wannan binciken ya yi daidai da wani tsohon bincike da aka haɗa kusan mutum 2,000 masu magana da harsunan Catalan da Sfaniyanci da ke koyon turancin Ingilishi: Cikin sauki matasan suka koyi harshen fiye da ƙananan yara.

A farkon wannan shekarar an yi wani bincike a jami'ar MIT ta Amurka wanda ya gano mutum 670,000 sun fi kwarewa idan suka fara koyon turancin Ingilishi tun suna ƴan shekara 10.

Mene ne amfanin koyon harsuna?

Mutane kan tambayi kansu. mene ne amfanin koyon wani harshen kasashen waje? Zan iya samun karuwar arziki? Zan kara wayewa? Zan sami karuwar lafiya?

Amma bincike ya tabbatar da cewa koyon yaren wata ƙasa na taimakawa wajen sadarwa da kulla zumunci tsakanin al'umomi.