Manchester City na son Alaba, Real Madrid za ta sayar da Jovic

Asalin hoton, Getty Images
KocinManchester City Pep Guardiola yana duba yiwuwar dauko dan wasan Bayern Munich daAustria David Alaba, mai shekara 28, a bazara. (Mirror)
Wakilin Kevin de Bruyne ya ce dan wasan na Belgium, mai shekara 29, ba zai bar Manchester City a bazarar nan ba, ko da kuwa an tabbatar da hukuncin haramta musu buga gasar Zakarun Turai. (Sporza - in Dutch)
Everton tanafuskantar gogayya a yunkurinta na dauko dan wasan Lille dan kasar Brazil Gabriel Magalhaes, mai shekara 22, bayan kungiya biyu a gasar Firimya ta nemi dauko dan wasan. (Sky Sports)
Arsenal tana so ta ci gaba da rike golan Argentina Emiliano Martinez, mai shekara 27, bayan ta soke shirinta na yin garambawul ga masu tsaron ragarta a bazarar nan. (Mirror)
Real Madrid tana shirin sauraren bukatar da za a shigar mata kan sayen dan wasan Serbia Luka Jovic, mai shekara 22. (Marca)
Leicester City ta yi amannar cewa za ta iya sayo Jovic a kan kusan £31m amma ba ta tuntubi wakilinsa ba tukuna. (Star)
Daraktan wasanninBorussia Dortmund Michael Zorc ya ce kungiyar ta fitar da jerin sunayen 'yan wasan da za su maye gurbin dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, idan ya bar su a bazara. (Kicker - in German)
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya shaida wa mahukunta kungiyar cewa yana son dauko dan wasan dan wasan gaba - kuma babban burinsa shi ne ya dauko Sancho - tare da dan wasan gaba da kuma dan wasan baya a bazara. (Telegraph - subscription required)
Liverpool za ta gurfanar da Fulham a kotu domin yanke hukunci kan kudin 'diyya' game da na Harvey Elliott. Dan wasan mai shekara 17 ya koma Liverpool a kakar wasan da ta wuce bayan kwangilarsa ta kare a Craven Cottage. (Liverpool Echo)
Real Madrid na shirin sayen'yan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 21, daga Paris St-Germain da Eduardo Camavinga, mai shekara 17, daga Rennes a2021 kuma ta gaya musu kada su sabunta kwangilolinsu a kungiyoyin da suke tamaula idan sun kare. (Sport - in Spanish)
Leeds na son dauko dan wasan Brighton Haydon Roberts, yayin da Brentford, Derby, RB Leipzig da kumaMainz suke son dauko dan wasan mai shekara 18. (Telegraph - subscription required)
Inter Milan tana son dauko dan wasanItaliya Emerson Palmieri, mai shekara 25, da dan wasan Faransa Olivier Giroud, mai shekara 33, daga Chelsea. (Goal)










