Man City da Juventus na son ɗauko Traore, Barca na zawarcin Ndombele da Ryan

Adama Traore

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Adama

Manchester City da Juventus sun sha gaban Barcelona a yunkurin dauko dan wasan Wolves dan kasar Sufaniya Adama Traore, mai shekara 24. (ESPN)

Chelsea ta fi samun dama wurin dauko dan wasan Bayer Leverkusen Kai Havertz, mai shekara 21, saboda kungiyoyi da dama sun ce ba za su iya biyan farashin da aka sanya kan dan wasan na Jamus, wato £90m ba. (Goal)

Barcelona ta nemi dauko 'yan wasan Tottenhambiyu; dan wasan Faransa Tanguy Ndombele, mai shekara 23, kuma dan wasan Ingila Ryan Sessegnon. (Evening Standard)

WatakilaTottenhamta bayar da aron Sessegnon a bazara a yayin da ake fargabar cewa ci gaban dan wasan mai shekara 20 na fuskantar koma-baya a hannun koci Jose Mourinho. (Telegraph)

Borussia Dortmund ta bai wa Manchester United wa'adin ranar 10 ga watan Agusta ta kammala sayen dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20. (Mirror)

Dan wasan gaba na Ingila Tammy Abraham, mai shekara 22, ya gaya waChelsea cewa yana son sabunta kwangilarsa inda za a rika biyansa £130,000 duk mako. (Times)

Kocin West Ham David Moyes yana duba yiwuwar zawarcin 'yan wasan Manchester Unitedbiyu Phil Jones, mai shekara 28, da kuma Jesse Lingard, mai shekara 27. (Independent)

Arsenal, West Ham da kumaEverton suna son dauko dan wasan Athletic Bilbao da Sufaniya Unai Nunez, dan shekara 23. (AS, via Sport Witness)

Tsohon dan wasan Ingila Daniel Sturridge yana son komawa kungiyar da ke buga Ligue 1 ko MLS. Dan kwallon mai shekara 30 yanzu haka ba shi da aikin yi. (L'Equipe - in French)

ShugabanBarcelona Josep Bartomeu ya ce zai yi wahala kungiyar ta sake dauko dan wasan Brazil Neymar, mai shekara 28, daga Paris St-Germain a bazara. (RAC1 - in Spanish)

Saint-Etienne tana sa ran rike dan wasan da ta aro daga Arsenal dan kasar Faransa William Saliba, mai shekara 19, domin ya buga mata wasan karshe na gasar French Cup, duk da sabani game da kara kudinsa ya zama £2.3m. (Mirror)

Dan wasan Netherlands Tahith Chong, mai shekara 20, zai iya barin Manchester United domin ya tafi zaman aro, a cewar wakilinsa. (Stretty News)

Barcelona ta tabbatar wa dan wasan Faransa Antoine Griezmann, mai shekara 29, cewa za ta rike shi har kakar wasa mai zuwa. (L'Equipe - in French)