Yadda macizai suka kashe fiye da mutum miliyan daya a Indiya cikin shekara 20

The son of an Indian snake charmer holds a cobra snake in Kapari village, around 40km southwest of Allahabad in Uttar Pradesh state, 25 July 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Akasari kububuwa da gamsheƙa da kasa ne macizan da suka kashe mutanen

An yi ƙiyasin cewa mutum miliyan 1.2 ne macizai suka kashe a Indiya a shekaru 20 da suka gabata a Indiya.

Kusan rabin waɗanda abin ya shafa na tsakanin shekaru 30 zuwa 69, sai kuma kwata ko kuma ɗaya bisa huɗu daga cikin waɗanda macizan suka kashe yara ne, a cewar binciken.

Akasari kububuwa da gamsheƙa da kasa ne macizan da suka kashe mutanen. Sauran mutanen da suka mutu wasu macizai ne har na'uka 12 suka haddasa kisan.

Akwai kisan da macizan suka yi da suka kasance masu muni sakamakon rashin asibiti a yankin da abin ya faru.

Rabin waɗanda macizan suka kashe sun mutu ne a lokacin damina tsakanin watan Yuni zuwa Satumba, wanda lokaci ne da macizai ke fitowa. Akasarin waɗanda suka mutu, macizan sun sare su ne a ƙafa.

Binciken wanda aka wallafa shi a jaridar open access journal eLife, manyan ƙwararru ne a ciki da wajen Indiya suka gudanar da shi. An yi shi ne bisa alƙaluman da aka tattara daga binciken da aka yi kan miliyoyin mutanen Indiya da suka mutu.

Kububuwa wadda macijiya ce mai haɗari da kuma faɗa ana yawan samunta ne a Indiya da kuma Kudancin Asia. Ta fi cin ɓeraye a matsayin abinci wanda hakan ya sa ta fi kusa da bil adama a ƙauyuka da birane.

Maciji
Getty
Cizon maciji a fadin duniya

  • Miliyan 5.4Yawan mutanen da aka yi kiyasin macizai na cizo duk shekara

  • 100,000Yawan mutanen da ke mutuwa sakamakon cizon maciji

  • 400,000Yawan mutanen da ke samun nakasa sakamakon cizon maciji

Bayanai: Hukumar Lafiya Ta Duniya

Gamsheƙa ta ƙasar Indiya akasari tana kai hari ne da dare kuma tana jawo mutum a rinƙa zubar da jini ta cikin jiki, wanda hakan na buƙatar kulawa ta gaggawa.

Binciken wanda aka gudanar tsakanin 2001 zuwa 2014, kashi 70 cikin 100 na mutanen da macizan suka kashe lamarin ya faru ne a jihohi takwas na ƙasar - Bihar da Jharkhand da Madhya Pradesh da Odisha da Uttar Pradesh da Andhra Pradesh (har da Telangana, wadda sabuwar jiha ce) Rajasthan da kuma Gujarat.

Masu binciken sun ce masu zuwa gonaki sun fi haɗarin samun sarin maciji musamman a lokaci irin na damina.

Sun ce yakamata a rinƙa ilmantar da mutanen wurin kan yadda za su rinƙa zuwa gonaki da kuma irin takalman da za su saka da safar hannu da kuma amfani da fitila domin rage haɗarin sarin maciji.

Hukumar Lafiya Ta Duniya ta bayyana cewa sarin maciji abu ne da ya kamata a mayar da hankali kansa a faɗin duniya.

Mutum 81,000 zuwa 138,000 ne ke mutuwa sakamakon sarin maciji a duk shekara a faɗin duniya. Kusan yawan irin mutanen nan ninki uku ne kuma ke samun sauƙi bayan sarin macijin da kuma samun naƙasa ta har abada.

Venomous Banded Krait snakes seen fighting among themselves on May 29, 2016 in Jalpaiguri, India.