Yadda maciji ya kashe daliba a cikin aji

Asalin hoton, AFP
A Indiya an dakatar da wani shugaban makaranta daga aiki bayan da wata daliba ta mutu a sanadin saran da maciji ya yi mata a cikin aji.
'Yan ajin yarinyar da iyayen dalibar mai suna Shehla Sherin suna zargi malaman makarantar da halin ko-in-kula da kuma rashin kai ta asibiti bayan da macijin ya sare ta.
Mutuwar yarinyar mai shekara 10 ya sa zanga-zanga ta barke inda wasu suka rika yin tattaki a garin Sulthan Bathery na jihar Kerala.
Hukumar da ke kula da ilimi a karamar hukumar ta kuma dakatar da wani mataimakin shugaban makarantar ranar Juma'a.
Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce a ranar Laraba da misalin karfe 3 na yamma agogon Kerala Sherin ta sanar da cewa macijin ya sare ta.
'Yan ajin su Sherin sun sanar da cewa wani malami wanda shi ma an dakatar da shi daga aiki, ya yi watsi da kukan da Sherin ke yi na maciji ya sare ta, duk da cewa daliban ajin sun yi ta nanata cewa a kai yarinyar asibiti.
Babu wanda ya kai Sherin asibiti har bayan sa'a guda - lokacin da mahaifinta ya isa makarantar domin daukan ta zuwa gida.
Iyalan yarinyar sun ce sun ziyarci asibitoci uku domin neman maganin dafin macijin, kafin ta mutu a kan hanyarsu ta zuwa asibiti na hudu.
Wannan mutuwar ta harzuka mutane a yankuna masu yawa a kasar, kuma sun rika mika kokensu kan rashin ingancin yanayin makarantun kasar.
Jami'an ma'aikatar ilimi na jihar ta Kerala sun umurci shugabannin makarantu da su tsaftace harabar makarantunsu.











