An gargadi mutane kan kifi mai kan maciji

Snakehead fish with an open mouth

Asalin hoton, United States Geological Survey handout

    • Marubuci, Daga Alejandra Martins
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo

"Idan kuna tunanin kifi mai kan maciji kuka kama, to kar ku sake shi ya tafi. Ku kashe shi nan take sai kuma ku sa a gidan kankara, don kuwa yana iya rayuwa ko ba a cikin ruwa ba."

Hukumar Kula da Albarkatun Kasa ce ta fitar da wadannan bayanai a jihar Georgia ta Amurka.

Wani kifi ne mai kan maciji da ake samun sa a arewacin Amurka da ake kira Channa argus. macijin yana da tsayi kuma ba shi da kauri. Bugu da kari,yana da hatsari.

Kwayaye dubu goma a shekara

Channa argus na cin duk wani abu da ya tari gabansa, kama daga sauran dangin kifaye, kwadi da kuma kaguwa.

Snakehead fish being measured

Asalin hoton, United States Fish and Wildlife Service handout

Kifin na da tsawon santi mita 80, yana kuma iya shakar iska da kuma yawo a sarari.

Hakan ya ba wa kifin damar yawo daga ruwa zuwa ruwa.

Matsawar kifin ya isa sabon wuri, to kuwa fada da shi na da matukar wahala. Macen kifin na saka kwayaye 10,000 a shekara.

Bazuwar kifi mai kan maciji

Ana samun kifi mai kan maciji a China da yankin Koriya, duk da a Amurka aka fara gano shi sama da shekaru 10 da su ka wuce.

Kawo yanzu nau'i hudu aka iya ganowa na kifin, an kuma yi amannar cewa kifin ya yadu ne a dalilin sayen shi da ake yi da nufin kiwata shi a cikin gidaje a cewar hukumomi a Amurka.

A man shows a stuffed specimen of snakehead caught in Philadelphia in 2005

Asalin hoton, Getty Images

Hakama ana samun kifi mai kan maciji a cikin daji a jihohin Florida da New York da Virginia da California da Massachusetts da kuma Maryland.

To amma a Maryland aka fara gano shi a shekarra 2012 kuma abun damuwa a lokacin shi ne irin yadda aka fahimci cewa ya bazu a cikin dazuka.

Neman taimako daga al'umma

Jami'ai a Jihar Georgia sun yi gargadi a ranar 8 ga watan Oktoba, bayan da wani masunci ya kama kifi mai kan maciji na farko a jihar.

Fishermen try to kill a snakehead fish in Florida

Asalin hoton, Getty Images

A gargadin, jami'an sun sanar da al'umma cewa kifin kan iya rayuwa a wajen ruwa, su kuma dauki hoton mataccen kifin da kuma inda suka kama shi.

Ya ya kifi mai kan maciji ke rayuwa a wajen ruwa?

Martin Genner, wani Farfesan kula da albarkatun ruwa da ke jami'ar Bristol da ke Burtaniya, ya fada wa BBC hanyoyin da kifi mai kan maciji ke amfani da su wurin rayuwa a doron kasa.

Snakehead fish near the surface

Asalin hoton, Getty Images

Farfesa Gennes ya bayyana cewa kifin na da wani wuri da yake shaka da fitar da iska idan ya fito sarari da masana ke kira 'suprabranchial chamber.'

Yana kuma da baiwar jan iska ya adana ta don yin amfani da ita cikin ruwa kamar yadda ake amfani da fanfon shakar iska a cikin ruwa.

Hunter looking for snakehead fish in the mud of a fried lake in India

Asalin hoton, Getty Images

Jan jiki

Kifi mai kan maciji na da damar yawo a kan kasa ya ja jiki don yin tafiya amma ba mai tsawo ba.

Kifin ya fi samun damar yin balaguro zuwa wani yanki a wuraren da ke da saurin bushewa ko kuma ba su samun ruwan sama sosai.

Catfish

Asalin hoton, Getty Images

Mr Gennes ya kara da cewa ba kifin mai kan maciji kadai ba ne mai yawo a sarari, akwai wasu dangin kifaye kamar nau'in kifi da ake kira 'Catfish', da kuma 'lungfish' da ke da wasu sassan jikin kifi mai kan maciji.

Akwai kuma wani dangin kifi da ake kira 'gouramies' da ke da wurin shakar iska da yawo a wajen ruwa na takaitaccen wuri..

Snakeheads in a crowded aquarium

Asalin hoton, Getty Images

Karfin da kifi mai kan maciji yake da shi ya sa yake iya mamaye abincin wasu halittun ruwa, kuma kifi ne mai karko da ya shiga gaban takwarorinsa da ke da hatsari amma ba su da karkon da yake da shi kamar na yawo ciki da wajen ruwa.

Kifi mai kan maciji na da ban al'ajabi, don har ta kai ana shiri na musamman kan kifin a tsahar namun daji, an kuma yi masa lakani da "Fishzilla"