Hajj 2020: Saudiyya ta haramta taɓa Ka'aba ga mahajjata

Ka'aba a Makka

Asalin hoton, Getty Images

Hukumomi a Saudiyya sun wallafa wasu ƙa'idojin kariya daga cutar korona ga mahajjatan da aka yarjewa sauke farali a bana.

Sabbin ƙa'idojin sun haɗa da haramta wa mahajjata taba Ka'aba yayin aikin Hajjin wanda ake ganin ya shafi hana taɓa Hajraul Aswad da ake taɓawa lokacin ɗawafi.

Za a bukaci mahajjata su riƙa ba da tazarar mita ɗaya da rabi yayin gudanar da ibadar sannan sanya takunkumi wajibi ne.

Miliyoyin musulmi ne daga sassan duniya ke gudanar da aikin Hajji sai dai a wannan shekarar an taƙaita adadin masu sauke faralin a karon farko kuma da ƙasar take haramta aikin Hajjin ga mahajjata na wasu ƙasashe.

A watan jiya ne ma'aikatar Aikin Hajji da Umara ta Saudiyya ta fitar da wasu sharuɗa guda takwas da suka shafi aikin hajjin 2020.

Su waye za su yi aikin hajjin bana?

Mutum 10,000 ne kawai za su yi aikin Hajjin bana amma mazauna Saudiyya kawai, ciki har da 'yan wasu kasashen da ke zama a can. Sai dai a baya can mazauna Saudiyya suna yin aikin Hajji ne kawai duk bayan shekara biyar.

Wannan layi ne

Ga dai sharuddan a jere kamar yadda ma'aikatar ta fitar:

  • Za a yi wa alhazan gwajin cutar korona kafin su fara aiki, sannan za a killace su bayan an kammala aikin.
  • Mazauna kasar da 'yan kasar 'yan kasa da shekara 65 ne kawai za su gudanar da aikin hajjin bana.
  • Ba za a bar mutanen da ke fama da munanan cututtuka kamar su ciwon suga da ciwon zuciya su yi aikin hajjin ba.
  • Za a dinga sa ido kan yanayin lafiyar kowane mahajjaci.
  • Za a dinga gudanar da ayyukan matakan aikin hajji rukunu-rukuni na mutane kadan-dkadan saboda tabbatar da dokar yin nesa-nesa da juna.
  • Yawan wadanda za su yi aikin hajjin bana ba za su haura 10,000 ba.
  • Babu wanda zai je Saudiyya don yin aikin hajji daga wasu kasashen.
  • Za a bude asibiti na musamman a Makkah don ayyukan gaggawa.
hajji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Miliyoyin mutane ke zuwa aikin hajji duk shekara daga kasashe daban-daban

Fiye da mutum miliyan biyu da dubu 500 ne suka gudanar da aikin Hajjin 2019 daga fadin duniya.

Wannan layi ne

Karin labarai masu alaka