Isa Ali Pantami: Da gaske ya saya wa matansa uku gidaje a Abuja?

Pantami

Asalin hoton, Facebook/NITDA

Bayanan hoto, Sheikh Pantami ya zama shugaban hukumar NITDA ne a shekarar 2016
Lokacin karatu: Minti 2

Ma'aikatar sadarwa ta Najeriya ta musanta labarin da wata jaridar intanet ta wallafa inda ta yi zargin cewa Minista Ali Isa Pantami ya saya wa matansa uku gidaje a Abuja.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma'aikatar Uwa Suleiman ta fitar ta ce wannan batu ba shi da tushe balle makama.

Sanarwar ta ce: "Labarin da jaridar intanet ta Sahara Reporters ta wallafa da ke zargin cewa ministan ya saya wa matansa uku gidaje a Abuja karya ne.

"Tun da ministan ya kama aiki a bai sayi gida ko daya ba, kuma gidan da yake zaune ciki ya kama shi ne tun a watan Janairun 2017, shekara biyu kenan gabanin ya kama aiki", in ji sanarwar.

Ta kara da cewa sauran gidaje biyun da jaridar ta wallafa bai ma san daga inda ta samo su ba.

Bugu da kari ta yi kira ga al'ummar kasar da su yi watsi da wannan kokarin bata wa Minista Ali Pantami suna da ake kokarin yi.

Sanarwar - wadda aka wallafa a shafin ma'aikatara sadarwa na Twitter - ta ce Pantami amintacce ne kuma kowa ya san matsayinsa na kyamar cin hanci da rashawa.

Ta kuma tunatar da al'ummar kasar cewa Ministan tsohon ma'aikacin jami'ar Madina ne, kuma ya dawo kasar nan ne domin ya bayar da tasa gudunmawar wanda hakan ke nuni da kishin kasar da yake da shi.

"Kudin da ake biyansa raguwa yayi idon aka kwatanta da abin da yake dauka a jami'ar da yake aiki da, mai zai sa ya zama mai handama," a cewar sanarwar.

Karin labarai da za ku so ku karanta: