Hotunan yadda matan Yarbawa ke kece kwalliya

Three models pose in A Ti De

Asalin hoton, Oye Diran

    • Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
Presentational white space

Wani mai daukar hoto dan Najeriya ya sake lalubo tsofaffin hotunan yadda matan Yarbawa ke kece ado tun a baya.

Short presentational grey line

Yayin da goggon Oye Diran ta tura mata wani tsohon hoton iyalinsa, ya yi matukar mamaki da zubin kwalliya da tsarin ado irin na matan Yarabawa a shekarun 1960 da 1970 da 1980.

Hoton na mahaifiyarsa ne da 'yar uwarta sanye da zane da rigar dinkin buba, wadanda suke shahararru ne a wajen matan Yarabawa a Najeriya.

Diran, wanda shi ma Bayarabe ne kuma ɗan Najeriya mai ɗaukar hotuna a birnin New York na Amurka, ya lura da yadda zane da riga suka sauya tsawon lokaci, amma da har yanzu shigar ta ci gaba da kasancewa mai daraja.

Three models pose in A Ti De

Asalin hoton, Oye Diran

Presentational white space

Sha'awar da shiga ta ba shi ta sa ya shiga internet laluben wasu kayatattun hotunan na tufafin Yarabawa mata, sai dai ya yi mamaki a abinda ya gani.

"Abinda na gani shi ne tufafin zamani da muta ke sanawa a yanzu, wanda ba shi nake bukata ba," kamar yadda ya shaida wa BBC.

Daga nan sai ya dauki kyamararsa ya samar da jirin hotuna da ya ambata A Ti De (wato mun iso).

Three models pose in A Ti De

Asalin hoton, Oye Diran

Presentational white space

Yarabawa sune kabila mafi girma ta biyu a Najeriya, da suka yi fice wajen gagarumin biki da shirya walima a kai a kai - kama daga na walimar suna zuwa ta gina sabon gida da ake yi gagarumin taron 'yan uwa da abokan arizki ana kade-kade ga abinci da kayan shaye-shaye.

Babban abinda ke takama da shi a lokacin bukukuwa shi ne sanya tufafi masu launi daban-daban.

Ga mata dai riga ce da zane, da a baya ake sanya su a kasan akwatu ana jiran biki na musamman.

Sai dai lokacin da ake tanadin irin wadancan kayan ya wuce, inda aka maye gurbinsu da anko, inda dukkan baki suke sanya kaya iri daya.

Wata alama dake nuna sauyi a yanzu ita ce, ba a ajiye irin wadannan kayan a kasan akwatun karfe, sai dai ana sanya su ne a can wata kuryar kwaba, kuma wajen da ba haske sannan ba a hada su da kayan da ake sanyawa yau da kullum. da ba su kai su muhimmanci ba.

"Adon Yarabawa ya ringa sauyawa ta fuskoki daban-daban cikin shekaru da dama da suka gabata, sai dai har yanzu sun ci gaba da rike kambunsu," kamar yadda Diran ya shida wa BBC.

Three models pose in A Ti De

Asalin hoton, Oye Diran

Presentational white space

"Ina ganin mun fara fuskantar sauye-sauye ne a bangaren daga farkon shekaun 2000 zuwa yau.

Misali, a shekarun 1960, tsawon zanen ba ya wuce gwiwa. Amma a yau tsawon zanen ya kan kai har tafin kafa. Mun ga tasirin nau'ikan wasu tsarukan sanya tufafi a kan ya Yarabawa," a cewarsa.

Model poses in A Ti De

Asalin hoton, Oye Diran

Presentational white space

An haifi Diran, kwararren mai zane-zane, kuma mai daukar hoto a birnin Lagos na Najeriya, mahaifiyarsa wata kwararriyar mai zane-zane ce kuma mahaifinsa likitan dabbobi ne kuma ɗan kasuwa ne.

"Mahaifiyarsa tana da shagon zane-zane a lokacin da muke yara, inda nake ganin tsofaffin ayyukanta, da kuma sababbin wadanda take yi.

Two models pose in A Ti De

Asalin hoton, Oye Diran

Presentational white space

"Na tashi kewaye da kayatattun zane-zane."

Two models pose in A Ti De

Asalin hoton, Oye Diran

Presentational white space

"Ina kokarin fito da kyawawan zane-zane da karfafawa jama'a gwiwa da kuma fito fito da akidoji a zane-zanena ," a cewarsa.

Three models pose in A Ti De

Asalin hoton, Oye Diran

Presentational white space

Tufafin Yarabawa ya zama wani sananne cikin shekaru, kama daga riguna masu fadi, da masu kwala da ma riguna masu fadin wuya.

Yadukan da ba sa sanyawa a baya yanzu sun zama sanannu, kuma kayan da ake yi masu fadi a da, a yanzu sun zama matsattsu.

Three models pose in A Ti De

Asalin hoton, Oye Diran

Presentational white space
Three models pose in A Ti De

Asalin hoton, Oye Diran

Presentational white space

"A Ti De kalma ce ta karfafa gwiwa," a cewarsa.

"Ana amfani da ita don sanar da zuwan wani ko kwata wajen gagarumin taro a mafi yawan lokuta."

Three models pose in A Ti De

Asalin hoton, Oye Diran

Presentational white space

Duka hotunan suna da hakkin mallaka