Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Sri Lanka: Me ya sa ake ƙona gawar Musulmin ƙasar?
- Marubuci, Daga Saroj Pathirana
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sinhala Service
Al'ummar Musulmi a Sri Lanka sun ce mahukunta na amfani da annobar korona wajen nuna musu bambanci da ƙyama ta hanyar tilasta musu ƙona gawar mamaci wanda haramun ne a addinin Islama.
A ranar 4 ga watan Mayu, Fathima Rinoza, wata uwar yara uku mai shekara 44 daga tsirarun Musulmi, an kwantar da ita a asibiti lokacin da aka yi zargin tana dauke da cutar Covid-19.
'Ƙullalliya' irin ta mahukunta
Fathima, da ke rayuwa a birnin Sri Lanka, Colombo, ta yi ta fama da matsalar numfashi, hakan ya sa mahukunta suka shiga fargabar ko ta kamu da korona.
A ranar da aka kwantar da ita a asibiti, mijinta, Mohamed Shafeek, ya ce wannan wata 'kulaliya ce' da aka shirya wa iyalansa.
''Yan sanda da sojoji da wasu jami'ai sun ziyarci gidana,'' a cewarsa.
''Sun hankada mu waje guda sannan suka yi mana feshi da kuma cikin gida. Duk mun tsorata amma ba su ce mana komai ba. Har jaririn watannin uku a duniya aka yi wa gwaji kafin daga bisani aka kwashe mu kamar karnaku aka killace mu.''
An garkame mu na dare guda sannan washe gari aka sake mu tare da umartar mu da mu killace kanmu na mako biyu.
A cikin wadanan kwanakin, muka samu sakon cewa Fathima ta rasu a asibiti.
Tilasta sanya hannu a takardu
An umarci babban ɗa ga Fathima ya je asibiti ko zai gane gawar mahaifiyarsa. Daga nan aka riƙe shi wa ba zai dawo gida ba saboda mutuwarta na da alaƙa da Covid-19.
Ya ce an tilasta masa sanya hannu a takardar amincewa a ƙona gawar mahaifiyarsa, duk da cewa hakan ya saba koyarwa addinin Musulunci.
''An shaida masa cewa akwai bukatar a cire wasu sassan jikinta domin yin gwaji. Me ya sa za su cire sassan jikinta in dai korona ce ajalinta?'' a cewar mahaifinsa Shafeek, wanda yake da yakinin ba a yi wa iyalansa cikakkun bayanai ba, kan ainihin abin da ya faru.
Iyalan Fathima sun bi sahun sauran al'ummar Musulmi a kasar wajen sukar gwamnati kan amfani da annobar wajen nuna wariya a garesu.
Sharuɗɗan WHO
Sun ce hukumomi na amfani da karfi wajen tilasta ƙona gawawwakin mutane da korona ta yi ajalinsu, duk da cewa ƙa'idojin WHO ba su ba da damar a binne mutumin da wannan cuta ta hallaka.
Sun ce wani sabin salon muzgunawa ce da cin zarafi daga ƙabilar Sinhalese masu rinjaye.
A watan Afrilu 2019, masu ikirarin jihadi da ake alakantawa da wata karamar kungiyar sun kai hare-hare a manyan otel-otel da coci-coci a Colombo da ke gabashin kasar, tare da kashe mutum sama da 250, ciki har da baki 'yan ƙasashen ƙetare.
Mummunan harin, da kungiyar IS ta dau alhaki, ya girgiza kasar. Musulmi da dama tun daga wannan lokaci suka shiga tsaka mai-wuya.
'Barazana'
Tun mutuwar Musulmi na farko dauke da wannan cuta a ranar 31 ga watan Maris, wasu kafafen yadda labaran suka fito ƙarara suna daura alhakin yaduwar cutar kan al'ummar Musulmi, duk da cewa mutuwar mutum 11 aka sanar a hukumance a kasar.
Dukkanin gawarwakin 11, har da Musulmin da ke cikinsu an ƙona su.
Dokta Sugath Samaraweera, babban jami'in gwamnatin kan annobar cutuka, ya ce tsarin gwamnati ne cewa duk wanda ya mutu sanadiyar Covid-19 da wayanda ake zargin ita ce ajalinsu, a ƙona su saboda binnesu na iya sake yada cutar ta hanyar ruwan sha.
Dokta Samaraweera ya ce kwararru sun sahale wannan tsarin ne domin kare al'umma.
Sai dai masu fafutika Musulmi, shugabannin al'umma da 'yan siyasa sun bukaci gwamnatin Sri Lanka ta sake nazarin matakinta.
'Kasa daya tilo'
Sri Lanka ita kadai ce ƙasa cikin mambobi 182 na WHO da ake ƙona gawawwakin Musulmi saboda korona, kamar yadda wani tsohon minista kuma me neman takara a zabe mai zuwa Ali Zahir Moulana ya gabatar a wani korafi.
Moulana ya shaidawa BBC cewa al'ummar Musulmin ƙasar za su amince da hukunci da gwamnati ta yanke ''indai aka tabbatar a kimiyance cewa binne gawa hadari ne ga lafiya''.
Kalamansa sun samu goyon-baya manyan shugabannin addinin Musulmin ƙasar wadanda suke cewa bayanai sun nuna ƙarara cewa babu wata hujja ko bincike kimiyya da ta tilasta ƙona gawa, kuma wannan mataki na gwamnati son-kai ne da kokarin raba kan ƙabilun kasar.
Ƙa'idoji mabambanta
A ranar da Fathima ta mutu, an samu wani mutum mai shekara 64 Abdul Hameed Mohamed Rafaideen da shi ya mutu a gidan 'yar uwarsa da ke Colombo.
Mutumin wanda lebura ne kuma uba ga yara hudu ya yi ta fama da matsalar numfashi.
Dan karamin dansa, Naushad Rafaideen, ya shaida wa BBC cewa wani makwabcinsu shi ma ya rasu a wannan ranar.
Saboda dokar ƙulle, 'yan sanda sun umarci iyalansa su kai gawarsa tare da ta mahaifinsu asibiti.
A mutuware wato inda ake killace gawa, likitoci sun shaida wa Naushad cewa ba shi da damar taba gawar mahaifinsa saboda barazanar korona, duk da cewa babu bayanai da ke tabbatar da cewa korona ce ajalinsa.
Fargabar barazana
Naushad, wanda bai iya karatu ba, an bukace shi ya sanya hannu a wata takardar amincewa a ƙona gawar mahaifinsa.
Naushad ya ce ba shi da tabbacin abin da zai same shi idan ya bijire, sai dai yana fargabar barazanar da 'yan uwansa za su shiga da sauran al'ummarsu idan ya nuna turjiya. Ba hakan ne kuma ya faru a kan makwabtansa ba.
Naushad da wasu tsirarun danginsa kadai aka amince su shaida yadda aka ƙona gawar mahaifinsa.