Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Yemen: Abu biyar da suka sa cutar korona ta ta'azzara a kasar
Annobar korona za ta iya yaduwa cikin gaggawa zuwa wurare masu nisa tare da yin mummunan tasiri na sanadin rayuka a Yemen sama da kowacce kasa a duniya, in ji Majalisar Dinkin Duniya.
1. Har yanzu ƙasar na fama da yaƙi
Tun 2015 Yemen ta fada cikin mummunan rikici, wanda ya janyo wa miliyoyin mutane rashin samun kulawar lafiya yadda ya kamata, babu ruwa mai kyau ga karancin tsafta a ko ina - wanda hakan zai kawo tarnaki kai tsaye ga yakin da ake da annobar.
An takaita shigar da abinci da magunguna tare da kayan jinkai zuwa wasu sassa, gamayyar da Saudiyya ke jagoranta ta toshe tashoshin wura da na sama a kasar da ke yaki da mayakan Houthi - yayin da suma kansu 'yan tawayen ke kawo tsaiko ga raba kayan agajin.
Rashin tsayayyar gwamnati ya sanya yaki da korona ya zama gagarumin abu a kasar.
2. Tuni kasar ke fama da matsalolimafi muni da suka shafi bil'adama a duniya:
Wannan yanayin da ake ciki zai iya haifar da cutuka masu yaduwa ga al'ummar kasar.
Kimanin shekara uku gabanin annobar korona Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana Yemen a matsayin wurin da ya fi bukatar taimako sama da ko ina a fadin duniya. Kimanin mutum miliyan 24 a kasar wadanda sune kaso 80 cikin 100 na 'yan kasar duk sun dogara ne a kan agajin da ake kai wa domin su rayu, yayin da wasu miliyoyin ke fama da yunwa.
Hasashen da aka yi ya nuna kimanin yyara miliyan 2 a kasar na fama da tamowa, kuma tuni kasar ke fama da yadda za ta kawo karshen cutuka irin su zazzabi Malaria da kwalara gabanin zuwa korona.
Rashin garkuwar jiki mai karfi saboda cuwuka irin kwalara na nufin annbar korona za ta iya kama marasa lafiyar cikin sauki, kuma za su sha matukar wuya kan su warke.
3. Dama tuni tsarin kiwon lafiyar Yemen ya rushe:
Yakin da aka kwashe shekara biyar ana yi ya kara durkusar da tsarin kiwon lafiyar kasar, abin da ya sanya ba za su iya shawo kan annobar korona ba.
An lalata asibitocin sama da 3,500 a yamen ko kuma an ruguza su sakamakon hare-hare ta sama, kadan ne ke aiki kamar yadda ya kamata.
Rahotanni na cewa asibitoci sun cika da mutane, kuma ga karancin ainihin magungunan da ake bukata - a kasar da ke da mutum sama da miliyan 27, na urar taimakawa numfashi da ake da su ba su fi daruruwa ba.
4. Har yanzu ba a san adadin masu cutar ba a kasar:
Ba tare da sanin takamaimai su wanene masu cutar ba, yana da wahala a iya kare yaduwarta ko kuma shiri kan yawan masu dauke da ita a kasar da dama tana cikin matsalar tsarin kiwon lafiya.
Tun lokacin da mutum na farko ya kamu da cutar a yankin da gwamnati ke iko da shi a watan Afirilu, sanin gaskiyar adadin masu cutar ya zama abu mai wuya.
Gwamnatin kasar ta ce akwai mutum 900 masu dauke da cutar, yayin da 'yan tawayen da ke zaune a yankin da ke da cin koson jama'a suka ce mutum hudu ne kawai ke dauke da cutar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce saboda boye gaskiyar da 'yan tawaye da kuma gwamnati ke yi ga kuma karancin kayan gwajin cutar, wannan ya tabbatar da cewa a kwai masu dauke da cutar sama da yadda ake sanarwa.
5. Su kansu ma'aikatan lafiya na cikin hatsari:
Tare da magani da za a rika bai wa marasa lafiyar, jami'an lafiyar na fama da karancin kayan kariya, kamar rigar da ake sanyawa lokacin aiki da takunkumin fuska da dai sauran kayan aikin da kan kare likitoci.
Wata majiya da ba'a tabbatar da ingancinta ba, ta ruwaito cewa gwamman ma'aikatan lafiya ne suka mutu a yankin da gwamnati ke ido da shi da kuma na 'yan tawayen sakamakon wannan cuta.
Daya daga cikin fitattun masana kan cutuka masu yaduwa a Temen, Yasin Wareth ya mutu sakamakon Covid-19 a farkon wannan watan, a wani abu da aka kira gagarumar asarar da bangaren lafiyar Yemen ya yi.