APC ta shiga ruɗani, Ganduje ya ja daga da kwamitin Buhari: Abubuwan da suka faru a Najeriya makon jiya

Asalin hoton, Nigeria Police force
An yi wa mutum 717 fyaɗe cikin wata biyar a Najeriya - Mohammed Adamu
Mata 717 aka yi wa fyaɗe cikin wata biyar a Najeriya, daga watan Janairu zuwa watan Mayun 2020.
Babban sufeton 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Litinin bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar, kamar yadda jaridar Premium Times da kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International suka ruwaito.
Wannan kalamai na Sufeton 'yan sandan na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan aka yi ta samun rahoton matan da aka yi wa fyaɗe a sassan kasar, al'amarin da ya harzuka mutane da dama.
Elrufa'i ya janye jami'an tsaro a kan iyakokin Kaduna

Asalin hoton, Twitter/@elrufai
A ranar ta Litinin ne gwamnatin Kaduna ta bayar da umurnin janye dukkanin shingayen da aka datse kofofin shiga jihar tare da ba jami'an tsaro umurnin su janye.
Sanarwar da aka wallafa a shafin Twitter na gwamnatin jihar ta ce za a toshe hanyoyin ne kawai lokacin da dokar hana fitar dare ta fara aiki daga karshe 8 na dare zuwa 5 na safe.
Sannan gwamnati ba za ta sake tura jami'ai ba a kan iyakokin jihar.
An yi zanga-zanga a Katsina kan kashe-kashe a Arewacin Najeriya

Asalin hoton, Coalition of Northern Youth
Kungiyoyi da dama ne suka fatsama kan tituna a birnin Katsina da ke arewacin Najeriya ranar Talata da safe inda suka yi kira a dauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.
Masu zanga-zangar, mai taken #ArewaIsBleeding a turance, wato 'Jini yana kwarara a Arewa', sun bayyana matukar bacin ransu kan halin ko-in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-kashe a yankin.
Sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohi 19 da ke arewacin kasar don matsa lamba ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan masu kashe-kashen.
Rahotanni sun nuna cewa makon da ya gabata kadai 'yan bindiga da mayakan Boko Haram sun kashe mutum fiye da 100 a hare-haren da suka kai jihohin Katsina da Borno.
Sai dai jim kadan bayan zang-zangar ne 'yan sanda suka kama Nastura Ashir Sharif, shugaban gamayyar kungiyoyin.
Sai dai an sake shi bayan ya shafe kwanaki biyu a hannun 'yan sanda sakamakon caccakar da wasu manyan Arewacin kasar suka yi wa Shugaba Buhari, ciki har da Alhaji Bashir Tofa.
Obaseki ya fice daga APC bayan ya gana da Buhari

Asalin hoton, Getty Images
A makon ne gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya fita daga jam'iyyar APC mai mulkin kasar bayan rikicin cikin gida tsakaninsa da shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomole.
Obaseki ya bayyanawa manema labarai bayan ganawarsa da shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja cewa zai koma wata jam'iyyar domin neman takara a wa'adin mulki na biyu.
A makon da ya gaba ce shi ne jam'iyyar APC ta ce Obaseki ba zai iya shiga takara a zaben fitar da gwani ba saboda a cewarta akwai bambamce-bambamce a takardun makarantarsa.
Ranar Juma'a Godwin Obaseki ya shiga jam'iyyar PDP domin "na samu cimma burina na sake lashe zaben gwamnan jihar Edo."
APC ta shiga ruɗani: Abiola Ajimobi ya zama shugaban riƙo

Asalin hoton, Twitter/@AAAjimobi
Sai dai jim kadan bayan ficewar Gwamna Obaseki daga APC, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya ta tabbatar dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar APC, saboda rashin kwararan hujjoji.
Hakan ne ya sa APC Jam'iyyar mai mulki a Najeriya ta bayyana Sanata Abiola Ajimobi a matsayin wanda zai maye gurbin Adams Oshiomhole, inda zai ci gaba da shugabancin jam'iyyar amma na riƙo.
Sakataren yaɗa labaran APC na ƙasa, Lanre Issa-Onilu a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce bayan tuntuɓar sashen harkokin shari'ah na jam'iyyar kuma bisa tanadin sashe na 14 ƙaramin sashe na 2, uku cikin baka na tsarin mulkin APC mataimakin shugabanta na ƙasa shiyyar kudu ne zai ci gaba da jagorantar APC a matsayin riƙo.
Ta ce matakin ya zo ne bayan kwamitin gudanarwar jam'iyyar APC ya samu labarin da ke nuna cewa kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Oshiomhole.
Sai dai wani babban dan jam'iyyar, Victor Giadom, ya samo umarni daga kotu inda ta amince ya zama shugaban riko na jam'iyyar lamarin da ya jefa ta cikin ruɗani.
Ganduje ya yi watsi da rahoton kwamitin Buhari kan mace-macen Kano

Asalin hoton, @KNSMOH
Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rahoton gwamnatin tarayyar kasar da ya gano cewa cutar korona ce ta yi ajalin kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen da suka mutu a baya bayan nan.
A wata sanarwa da ya fitar, Abba Anwar, mai magana da yawun Gwamna Ganduje, ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin yin bincike kan mace-mace ya gano cewa kusan kashi kashi goma sha shida cikin dari ne suka mutu sanadin korona.
Gwamnan ya ambato kwamitin yana cewa: "Mutum 255 cikin 1604 da suka mutu, wato kashi 15.9... ne suka mutu sanadin cutar korona. Wasu daga cikin mace-macen suna da alaka da rashin samun magunguna da kuma dakatar da harkokin rayuwa da na kasuwanci saboda fargabar annobar korona."
A makon shekaranjiya ne Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano ya nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan sanadin mace-macen da ba a saba gani ba a jihar.












