Godwin Obaseki: Gwamnan Edo ya shiga jam'iyyar PDP

Obaseki da Oshimohle
Bayanan hoto, Obaseki da Oshimohle sun dade suna kai ruwa rana
Lokacin karatu: Minti 1

Gwamnan jihar Edo da ke kudancin Najeriya Godwin Obaseki ya koma jam'iyyar PDP.

Gwamna Obaseki ya bayyana shiga jam'iyyar ta PDP ne ranar Juma'a da rana a sakatariyar jam'iyyar da ke Benin, babban birnin jihar, kamar yadda PDP ta wallafa a shafinta na Twitter.

Ya shiga jam'iyyar ne kwana kadan bayan ya fice daga jam'iyyar APC wacce a cikinta aka zabe si a karon farko.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Gwamnan ya ce ya shiga PDP domin "na samu cimma burina na sake lashe zaben gwamnan jihar Edo."

A makon da ya wuce ne jam'iyyar APC ta ce Obaseki ba zai iya shiga takara a zaben fitar da gwani ba saboda a cewarta akwai bambamce-bambamce a takardun makarantarsa.

Sai dai masu lura da harkokin siyasa na ganin rikicin ubangida da yaronsa da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Adams Oshimohle kuma shugaban APC da kotu ta dakatar ne ya yi sanadin hana shi sake takara.

Ranar Talata Gwamna Obaseki ya fita daga jam'iyyar APC bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja yana mai cewa zai koma wata jam'iyyar domin neman takara a wa'adin mulki na biyu.

A makon da ya wuce ne jam'iyyar APC ta ce Obaseki ba zai iya shiga takara a zaben fitar da gwani ba saboda a cewarta akwai bambamce-bambamce a takardun makarantarsa.