Ana zargin mahaifi da cin zarafin 'yarsa mai shekara bakwai a Nigeria

Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Oyo ta ce gwamnatin jihar ta ceto wata yarinya 'yar shekara bakwai, wadda mahaifinta ya riƙa cin zarafinta ta hanyar duka da gallazawa.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Kwamishina Alhaja Faosat Sanni tana siffanta lamarin da "dabbanci ga ƙaramar yarinya" a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a.

Kwamishinar ta ce an kama mahaifin ne bayan kwamitin karɓar ƙorafe-ƙorafe kan lalata da cin zarafi na ma'aikatarta ya samu rahoto.

Ta ce: "Mun samu rahoton cin zarafin ne ta kafar sada zumunta na wani da ke zaune a yankin."

Ta ci gaba da cewa: "Ana zargin mahaifin yarinyar da ke zaune a Bodija na birnin Ibadan da zargin ji wa 'yarsa ciwo, wadda sakamakon haka ta samu tabo da kumburi a jikinta.

"Sannan an rawaito cewa mutumin wanda yake aikin gadi, yana azabtar da yarinyar bisa dalilin da har yanzu ba a kai ga ganowa ba.

"Kazalika mun samu labarin cewa mahaifiyarta ta tafi garinsu a Jihar Akwa Ibom domin ta haihu, inda ta bar wa mijinta yarinyar."

Kwamishinar ta ƙara da cewa an kai yarinyar asibitin yara na Oni and Sons da ke Ibadan domin duba lafiyarta, yayin da ma'aikatar ke niyyar ba ta duk tallafin da ya dace.