Boko Haram ta kashe mutum 69 a Borno, 'Yan bindiga sun hallaka 30 a Katsina

Rahotanni daga jihohi biyu na arewacin Najeriya na nuna cewa an kashe farar hula kusan 100 a hare-haren da aka kaddamar kan al'umma a jihohin Borno da Katsina.
A arewa maso gabashin kasar, wani hari da mayaka masu da'awar kishin addinin Islama suka kai jihar Borno ya halaka mutum kimanin 69.
Wadanda lamarin ya faru kan idanunsu sun ce mayakan 'yan kungiyar ISWAP - wani tsagi na Boko Haram sun kutsa kauyen Gubio inda suka budewa jama'a wuta tare da bi ta kan wasu al'ummar garin.
Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun yi awon gaba da shanu da kuma rakuma.
Yankin na Gubio ya sha fuskantar irin wadannan hare-hare lamarin da ya sa al'ummar yankin suka yi shirin ko ta kwana domin kare kansu.
A yankin arewa maso yammacin kasar, mazauna yankin sun shaidawa BBC cewa an kashe mutum fiye da 30 a hare-haren 'yan bindiga a kauyen Kadisau da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Bayanai sun nuna maharan sun far wa garin ne da yammacin ranar Talata inda suka kwashe awanni suna cin karensu babu babbaka.
Wannan hari dai na zuwa ne sa'o'i kasa da 10 bayan da wasu matasa suka gudanar da zanga-zangar nuna takaici dangane da hare-haren 'yan bindiga a kauyen 'Yantumaki da ke karamar hukumar Danmusa a jihar ta Katsina.
'Boko Haram ta gagari kundila'

Asalin hoton, Getty Images
An shafe fiye da shekaru 10 hukumomi a Najeriya suna yaki da kungiyar Boko Haram - wacce ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da lalata dukiya ta miliyoyin naira.
Rikicin na Boko Haram wanda aka soma a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya fantsama zuwa bakwabtan kasashe kamar su Nijar, Chadi da kuma Kamaru.
Gwamnatin Buhari dai ta dade tana ikirarin karya lagon kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin arewa maso gabas, amma kuma har yanzu mayakan kungiyar na ci gaba da yi wa mutanen yankin barazana.











