Coronavirus: 'Boko Haram na iya yaɗa korona a ƙasashen Tafkin Chadi"

Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoto ya yi iƙirarin cewa tafiye-tafiyen da mayaƙan Boko Haram ke yi tsakanin ƙauyuka da garuruwan da ke kan iyakokin ƙasashen Yankin Tafkin Chadi na iya zama wata kafa ta yada cutar korona.
Ya ce duk da hana zirga-zirga da gwamnatoci suka yi, amma 'yan ƙungiyar na ci gaba da harkokinsu daga wannan gari ko wannan ƙauye zuwa wancan.
"Kuma idan suka ci gaba da waɗannan tafiye-tafiye, to za su iya ɗaukar cutar daga wannan al'umma su kai wa wata.
Ko dai su yi a cikin ƙasa guda ko ma su ɗauka daga wata ƙasa su kai wa wata ƙasa tun da dai suna shiga cikin al'umma kuma ta yiwu ko a cikinsu ko cikin al'ummar a samu wanda ya kamu (da korona)."
Rahoton wanda Gidauniyar Tony Blair ta fitar ya yi nuni da cewa hatta a sansanin 'yan gudun hijira na Pulka, an samu mutumin da ya rasu sanadin korona, don haka ba abin mamaki ba ne a samu ƙauyukan da cutar ta shiga.
Audu Bulama Bukarti, wani mai bincike kan ayyukan ƙungiyoyin ta'addanci a Afirka da ke aiki da Gidauniyar Tony Blair ya ce ci gaba da zirga-zirgar Boko Haram, ɗaya ne daga cikin hanyoyin da bincikensu ya gano ƙungiyar za ta iya kawo cikas ga yaƙi da wannan annoba da ta gallabi duniya.
A Najeriya kawai ya zuwa yanzu cutar korona ta kashe sama da mutum 200, baya ga masu fama da cutar sama da 7,000 da hukumomi suka gano.
Ya ce: "Mun san cewar suna fitar da bidiyo da hotuna da ke nuna yadda suke shiga ƙauyuka a cikin Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi suna abin da suke kira wa'azi da kuma dabbaƙa shari'ar Musulunci@.
Mai binciken ya kuma ce wata hanya da Boko Haram za ta iya kawo cikas a yaƙi da annobar korona, ita ce wajen yaɗa bayanan ƙarya.
Rahoton ya ce tun bayan ɓullar cutar tsagin Boko Haram ƙarƙashin jagorancin Abubakar Shekau ya fitar da bidiyo har sau biyu ko uku.

Asalin hoton, AFP
"Kuma a ciki yana yada bayanan ƙarya waɗanda ba su dace da abubuwan da jami'an lafiya har ma da malaman addinin Musulunci suka suka yi furuci a kai ba."
Audu Bukarti ya ce zargin da Shekau ya yi cewa ana amfani da annobar don hana musulmai yin addininsu, da sallolin jam'i da Juma'a, bayanan ƙarya ne da za su iya shafar yadda gwamnatoci ke yaƙi da korona.
A cewarsa duk da yake ƙungiyar Boko Haram ba ta da goyon bayan al'umma, amma idan aka ci gaba da samun bayanan ƙarya irin waɗannan, hakan zai dada ƙarfafa kokwanton da wasu ke shi game da ita kanta cutar.
Rahoton ya kuma lura cewa ta hanyar ci gaba da kai hare-hare a daidai wannan lokaci na annoba, lamarin na iya raba hankulan hukumomi wajen yaƙi da annobar.
"Kamar ɓangaren IISWAP sun yi muƙala mai tsawo a mujallar ƙungiyar ISIS inda a ciki suka ba da bayanin yadda za su riƙa amfani da jan hankalin hukumomi da cutar ta yi wajen kai hare-hare," in ji mai bincike.










