George Floyd: Yadda aka yi jana'izar baƙar fatar da 'yan sanda suka kashe

An kammala jana'izar baƙar fatar nan George Floyd, wanda mutuwarsa a hannun 'yan sandan Amurka ta jawo zanga-zanga a faɗin duniya.

An dai binne shi ne a mahaifarsa da ke Houston inda dubban mutane suka halarci jana'izar tasa.

Kafin binne shi sai da aka ɗauki gawarsa daga wata coci da aka ajiye domin mutane su samu ganinta sannan daga bisani aka kai shi makabarta inda aka binne shi a kusa da kabarin mahaifiyarsa wadda ya ke kukan rabuwarsu.

Tunda farko a wajen taron addu'oin Mr Floyd, 'yan uwa da iyalai da shugabannin addinai da ma 'yan siyasa sun yi kiran da a kawo sauyi a kan irin cin kashin da ake yi wa bakaken fata a Amurka tare da neman a yiwa Mr Floyd adalci a game da kisan da aka yi masa.

Mista Floyd ya mutu a Minneapolis da ke Amurka a watan da ya gabata bayan wani ɗan sanda farar fata ya maƙure masa wuya da gwiwarsa na tsawon minti tara.

Kisan nasa ya janyo zanga-zanga a fadin duniya inda aka rinka nuna kyama a kan irin abin da aka yi masa tare da kiran a bi masa hakkinsa.

Dan takarar jam'iyyar Democrat Joe Biden na daga cikin wadanda suka halarci jana'izar Mr Floyd inda har ya ce "Duk sanda aka yi wa George Floyd adalci lokacin ne za mu samu adalci a tsakanin ƙabilun Amurka".